Mawaƙi Kizz Daniel ya musuluta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rahotanni daga kafafen sada zumunta na nuna cewa fitaccen mawaƙin Nijeriya, Kizz Daniel, ya sauya addininsa daga Kiristanci zuwa Musulunci, lamarin da ya janyo cece-kuce da kuma martani daga masoya a sassa daban-daban na duniya.

Wannan rahoto na zuwa ne watanni bayan wani fitaccen mawaƙi kuma wanda ya lashe kyautar Grammy, Burna Boy, ya bayyana a fili cewa shi ma ya karɓi addinin Musulunci. Wannan jerin sauye-sauyen da wasu fitattun jaruman mawaƙa ke yi ya ƙara jan hankalin jama’a kan tasirin addini a rayuwar shahararru.

Kizz Daniel, wanda aka haife shi da suna Oluwatobiloba Daniel Anidugbe, an san ya taso ne a ƙarƙashin tarbiyyar Kiristanci, duk da cewa asalin iyalinsa Musulmai ne. Rahotanni na nuna cewa sunan Musuluncinsa shi ne Dhikrullah, abin da ke ƙara nuna alaƙarsa da addinin Musulunci tun daga asali.

Mawaƙin na da ƙanin da ya yi kama da shi sosai, Uthman Anidugbe, wanda ke aiki tare da shi a harkokinsa na waƙa. Wannan kusanci na gida ya kasance wani ɓangare na rayuwarsa da ke janyo sha’awar masoya.

A baya-bayan nan, Kizz Daniel ya ƙara jawo hankalin jama’a bayan da ya yi tsokaci kan wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda wani ɗan Masar da wani zan Iraki ke kiran salla da muryoyi masu ratsa zuciya. Mawaƙin ya nuna sha’awarsa da bidiyon ta hanyar rubuta kalmar Larabci “Mashallah”, alamar girmamawa da jin daɗi a al’adance tsakanin Musulmai.

Duk da cewa, babu wata sanarwa a hukumance daga Kizz Daniel kansa kan sauyin addinin, wannan lamari ya ci gaba da zama abin tattaunawa, inda wasu ke ganin hakan a matsayin zaɓin kai tsaye na addini, yayin da wasu ke kira da a mutunta sirrin imani da zaɓin kowane mutum.

By ukarofi