Ribas: Wike ya zargi Fubara da karya yarjejeniyar sulhu na Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sabon tashin hankalin siyasa na neman ɓarkewa a Jihar Ribas, bayan Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya zargi Gwamna Siminalayi Fubara da karya yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙulla domin kawo ƙarshen rikicin siyasar da ya daɗe yana girgiza jihar.

Rahotanni sun nuna cewa Wike ya yi wannan zargi ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar godiya da ya kai ga al’ummar ƙaramar Hukumar Tai, inda ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai fito fili ya bayyanawa jama’ar Ribas cikakkun bayanai kan yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsa da gwamnan a gaban Shugaban ƙasa.

Taron sirri da Shugaba Tinubu ya jagoranta a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja a watan Yunin 2025 ya kasance wani yunƙuri na kawo ƙarshen rikicin iko tsakanin manyan jiga-jigan siyasar Ribas biyu. Rikicin ya kai ga durƙusar ayyukan gwamnati, sannan ya janyo ayyana dokar ta-ɓaci tare da dakatar da gwamnan da kuma ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas.

Bayan kammala taron na Abuja, Wike da Fubara sun fito a bainar jama’a suna bayyana aniyarsu ta yin aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar mai arzikin man fetur. Sai dai ba a bayyana sharuɗɗan yarjejeniyar ba, lamarin da ya bar ‘yan ƙasa cikin ruɗani da shakku kan ɗorewar sulhun.

Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a Tai, Wike ya ce Gwamna Fubara ya gaza cika muhimman sassan yarjejeniyar, yana mai bayyana hakan a matsayin cin amana da rashin gaskiya a siyasa. Ya ce, karya alƙawari a gaban Shugaban ƙasa ba ƙaramin abu ba ne, yana kuma tambayar yadda za a amince da wanda ba ya tsayawa kan abin da aka yarda da shi.

Wike ya kuma yi barazanar cewa ɓangarensa a siyasa ya shirya tsaf domin fuskantar duk wani sabon ƙalubale. Ya jaddada cewa ba kuɗi ke lashe zaɓe ba, illa goyon bayan jama’a, yana mai cewa sun taɓa doke masu kuɗi a baya kuma za su iya sake yin hakan.

A yayin jawabin, tsohon gwamnan Ribas ya yaba wa al’ummar Tai bisa goyon bayan da suka bai wa Shugaba Tinubu a zaɓen 2023, yana mai cewa wannan biyayya ta haifar da fa’idoji a zahiri, ciki har da muƙaman tarayya, ayyukan more rayuwa da kuma kafa Jami’ar Tarayya ta Muhalli a yankin.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Gwamna Siminalayi Fubara ko gwamnatin Jihar Ribas ba su fitar da wata sanarwa ba domin mayar da martani ga zargin da Wike ya yi ko barazanar bayyana yarjejeniyar da Shugaba Tinubu ya jagoranta.

Wannan sabon zazzafar magana ta Wike ta ƙara tayar da hankula, tare da haifar da fargabar cewa sulhun da aka cimma a Ribas na iya rushewa, abin da ka iya jefa jihar cikin sabon yanayi na rashin tabbas da rikicin siyasa.

By ukarofi