Sabon ciyaman a Kano ya yi barazanar sauka daga kujerarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Abubakar Muazu Mojo ya yi barazanar ajiye aikinsa na shugabancin ƙaramar hukumar muddin ba’a sauya masa Daraktan Mulki, wato DPM ba.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni ciyaman ɗin ya bada umarnin rufe ofishin DPM ɗin, wato Danjuma Zubairu Bebeji.

A wani saƙon murya da Mojo ya aika wa manema labarai, ya yi ikirarin cewa idan har Daraktan Mulkin bai bar ƙaramar hukumar ba, to shi zai bar masa wajen.

Ya kuma ce manufofin DPM ɗin sun saɓa da tsarin Kwankwasiyya na yi wa jama’a hidima da taimako.

Rahotanni sun bayyana cewa Mojo da DPM ɗin sun jima su na takun-saƙa tun lokacin da ya ke shugaban riƙon ƙwarya a karamar hukumar kafin a zaɓe shi a watan Oktoba.

Daga cikin zarge-zargen da Mojo ke yi wa Bebeji, akwai yi wa ƙaramar hukumar zagon-ƙasa da hana tafiyar da aiki yadda ya kamata, gami da sakaci a wajen aikinsa da hakan suka sa wasu mahimman takardu su ka ɓata.

Saboda haka ne Mojo ya ce idan ba a ɗauke Bebeji ba, to shi da majalisar kansilolinsa za su sauka su bar masa wajen.

Wakilinmu ya yi ta ƙoƙarin jin ta bakin Zubairu Bebeji, sai dai har zuwa lokacin haɗa rahoton nan bai ce uffan ba game da lamarin.