Safarar miyagun ƙwayoyi: Abba kyari da mataimakansa sun shiga hannu

Daga BASHIR ISAH

Bayan bada sanarwar neman DCP Abba Kyari da hukumar NDLEA ta yi da wasu ‘yan sa’o’i ne ‘ya sanda suka bada sanarwar Kyari ya faɗa a komarsu.

A jiya Litinin NDLEA ta yi shelar tana neman Abba Kyari ruwa a jallo bisa tuhumarsa da hannu cikin badaƙalar safarar miyagun ƙwayoyi, bayan da ya ƙi amsa mata gayyata don amsa mata tambayoyi.

Bayanai daga mai maganaa da yawun NDLEA, Femi Babafemi, sun nuna ‘yan sanda sun kama tare da miƙa musu DCP Abba Kyari, tsohon kwamandan rundunar IRT.

Jami’in ya ce an miƙa Abba Kyari ne tare da wasu mutum huɗu wanda su ma ake zargi da hannu a badaƙalar.

Waɗanda lamarin ya shafa su ne: DCP Abba Kyari; ACP Sunday Ubua; ASP Bawa James; Inspector Simon Agirgba da kuma Inspector John Nuhu waɗanda baki ɗayansu ‘yan sanda sun damƙe su sun kuma hannunta su ga babban ofishin NDLEA da ke Abuja da yammacin jiya Litinin don amsa tambayoyi da kuma ci gaba da bincike.

Da ma dai Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Usman Baba, ya yi kira ga shugaban NDLEA na ƙasa, Brig-Gen Buba Marwa (mai murabus) da ya gaggauta kama jami’an da ake zargi da taimaka wa Abba Kyari a harƙallar safar miyagun ƙwayoyi.

Babafemi ya ce: “NDLEA na bada tabbacin cewa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da waɗanda aka kama da ma waɗanda za a kamo nan gaba sun fuskanci fushin hukuma daidai da laifin da suka aikata bayan kammala bincike.