Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Shugaban hukumar nan dake yaƙi da sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa reshen yankin Keffi, hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa ACN Michael Bitrus Emmanuel, ya buƙaci sarakuna da shugabannin addinai da sauran shugabanni a duka matakai da jama’a bakiɗaya musamman waɗanda ke yankin su tabbatar suna haɗa kai da hukumar a ƙoƙari da suke yi don tabbatar da cigaba da nasara akan masu mu’amala da miyagun ƙwayoyi a yankin na ƙaramar hukumar Keffi da kewayen ta dama jihar bakiɗaya.
ACN Michael Bitrus Emmanuel ya yi wannan kira ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu game da harkokin hukumar a ofishinsa dake hukumar a Keffi a makon da ake ciki.
Ya ce tabbas kiran ya zame wajibi kasancewa duka nasarori da hukumar ke cimmawa a yanzu a yaƙi da masu harkar miyagun kwayoyin ba zai yiwu ba ba tare da cikakken goyon baya da haɗin kan al’umma baki ɗaya ba.
Ya ce idan al’umma za su riƙa ɓoye ingantattun bayanan sirri da za su taimaka wa hukumar wajen cafke masu aikata laifin to ba shakka za a samu cikas a fafatawar.
Shugaban hukumar na yaƙi da sha da kuma fataucin muggan ƙwayoyin a shiyyar ta Keffi ACN Michael Bitrus Emmanuel ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana cewa a cikin kimanin watanni 2 kacal da yayi a matsayin sabon shugaban rundunar na shiyyar hukumar ta cimma ɗimbin nasarori da suka haɗa da kamo da ƙwato wasu miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi da sauransu da yawa a lokutan sintiri na musamman da jami’an sa suke kai lungu-lungu da saƙo-saƙon yankin baki ɗaya ba dare ba rana inda ya sha alwashin cigaba da wannan ƙoƙari.
Sai dai da yake bayyana wasu daga cikin kalubalai da hukumar a shiyar ta Keffi ke fuskanta a yanzu ayayin da suke gudanar da harkokin su ACN Michael Bitrus Emmmanuel ya bayyana cewa wadannan matsaloli sun hada da rashin isheshen ababen hawa kamar mota da babura da sauransu da rashin issheshen masutguni wa jami’an hukumar a yankin da sauran su duk da cewa acewarsa akwanakin baya ya sanar da maimartaba sarkin Keffi Alhaji Shehu Chindo Yamusa game da batun inda ya tabbatar masa cewa za a yi wani abu game da hakan nan ba da dedewa ba.
Ya buƙaci gwamnatoti a duka matakai da sauran hukumomi da ƙungiyoyi dama masu hannu da shuni su rika tallafa wa hukumar da wadannan kayayyakin aiki don basu damar aiwatar da ayukan su yadda yadace.
Har ila yau ACN Michael ya kuma yi amfani da damar inda ya yaba wa kyakkyawar dangantaka dake tsakanin duka hukumomin tsaro a yankin inda yace a yanzu haka suna aiki ne tareda a yankin kana ya kuma yaba wa shugaban hukumar NDLEA din na jihar ta Nasarawa baki daya game da aiki tukuru da yake yi don tabbatar an rage ko shawokan wadannan miyagun mutane cikin al’umma a jihar dama ƙasa baki daya.
Sabon shugaban hukumar NDLEA na shiyar Keffi din ACN Michael Bitrus Emmanuel dai ya maye gurbin tsohon shugaba Ndubuisi Chukuemeka ne kuma tunda yanzo cikin watanni 2 kacal al’umma suke ta yaba masa game da ƙoƙarinsa na daƙile harkokin miyagun ƙwayoyi a yankin kawo yanzu.
