Sai da JAMB za a samu gurbin karatu a NDA – Hukumar Makaranta

Daga WAKILINMU

Makarantar Horas da Sojoji ta Nijeriya (NDA) ta ce hankalinta ya kai kan wani rahoton ƙarya da ke ta karakaina a soshiyal midiya game da cewa an dakatar da JAMB a tsarin ɗaukar ɗalibai na ’73 Regular Course’.

Da wannan makarantar ta wayar da kan al’umma cewa lallai sai da shaidar jarabawar UTME za a iya samun gurbin karatu a ’73 Regular Course’, bayan kuma an samu adadin makin da hukumar JAMB ta tsayar.

Daga nan, makarantar ta shwarci jama’a da su yi watsi da rahoton ƙaryar da aka yaɗa wanda ya nuna wai an dakatar da JAMB daga tsarin neman gurbi a ’73 Regular Course’. Tana mai cewa rahoton ba shi da tushe balle makama.

Ta jaddada cewa bayanin bogen ba shi da wata alaƙa da NDA, ta ce za ta hana duk wani ɗalibi da bai cika wannan sharaɗi ba gurbin karatu.

Haka nan ta ce duka harkokinta da take gudanarwa a bayyane suke kuma tana wallafa dukkan bayanan da al’umma ke buƙatar sani a shafinta na intanet: www.nda.edu.ng haɗa da wasu manyan jaridun ƙasar nan.

Don haka ta ce tana shawartar masu neman gurbin karatu a NDA da su riƙa bibiyar shafinta na intanet da aka bayar da adireshin a can sama domin samun sahihan bayanai.

Duka waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin takardar sanarwar manema labarai da hukumar NDA ta fitar ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a, Major Bashir Jajira.