Imo: An sako sarki da fadawansa da aka yi garkuwa da su

Daga AISHA ASAS

Bayanan da Manhaja ta samu ba da jimawa ba daga jihar Imo, sun nuna an sako Sarkin Umueze Nguru Aboh a ƙaramar hukumar Mbaise, Eze Charles Iroegbu yare da fadawansa.

Talatar da ta gabata wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi garkuwa da Eze Iroegbu tare da wasu fadawansa su bakwai a kan hanyarsu ta zuwa wajen ɗaurin aure a ƙaramar hukumar Isiala Mbano.

Binciken Manhaja ya gano cewa da sanyin safiyar wannan Asabar ne basaraken da fadawansa suka iso gida.

Wata majiya ta kusa da fadar sarkin ta shaida cewa waɗanda lamarin ya shafa sun dawo gida lafiya kuma jama’a sun karɓe su hannu bibbiyu cike da murnar ganin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *