Sallah: Kwankwaso ya karɓi baƙuncin Obi, Makinde da Seriake Dickson a Kano

Spread the love

Wasu jiga-jigan adawa a siyasar Nijeriya sun kai wata ziyara a gidan jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Lahadi.

Daga cikinsu akwai tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da gwamnan Oyo Seyi Makinde da kuma Sanata Seriake Dickson da dai sauransu.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya ce ƴan siyasar sun kai masa ziyarar gaisuwar sallah ne.

Kwankwaso, wanda ke jam’iyyar NNPP mai hamayya – ana tunanin zai sauya sheƙa zuwa wata jam’iyyar, bayan da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP zuwa APC mai mulki.

A cikin watannan ne dai Peter Obi ya sanar da komawarsa ADC a hukumace, yayin da gwamnan Oyo Makinde ya kasance gwamna na biyu bayan na Bauchi da suka rage a jam’iyyar PDP.

By Babaji