Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana goyon bayansa ga manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf na bunƙasa ilimi, ƙarfafa matasa da ci gaban gine-gine.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gaisuwar Sallah ta hawan Nassarawa da ya kai fadar gwamnati a ranar Lahadi, inda ya yaba wa gwamnatin bisa shirye-shiryen tallafin karatu da bunƙasa matasa.
Ya kuma ce Masarautar Kano za ta ci gaba da marawa gwamnati baya domin inganta rayuwar al’umma, tare da bayyana cewa ya koma makaranta domin karatun lauya don zama abin koyi ga jama’a.
A nasa ɓangaren, Shugaban majalisar dokokin Jihar, Ismaila Jibril, wanda ya wakilci gwamnan, ya ce goyon bayan Sarkin na ƙara ƙarfafa gwiwar gwamnati.
Ya kuma buƙaci al’umma da su zauna lafiya, su riƙe haƙuri da juna, tare da bai wa yara tarbiyya nagari, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma samar da ababen more rayuwa.
