Al’ummar Yarabawa na Nyanya Gwandara sun yi wa Isa Kogi wankan sarautar Oba-Teru

Spread the love

Daga JOHN DOGO WADA a Keffi

Al’ummar Yarabawa da ke yankin Nyanya Gwandara a ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa sun yi wa sarkin baki na Masaka wato Alh. Isa Kogi wankan sarautar su na musamman da suke kira Oba-Teru na wannan yankin su baki ɗaya.

An gudanar da gagarumin bikin wankan sarautar ne a layin Osama dake garin Masaka ranar La’adi na mako da ake ciki.

A jawabin sa jim kaɗan kafin a naɗa sarautar a hukumance, shugaban al’ummar Yarabawa na Nyanya Gwandaran, wato Alhaji Ibrahim Agesinkara bayan ya taya sabon Oba-Teru nasu ɗin murnar babbar sarautar ya kuma bayyana cewa duka al’ummar Yarbawa na Nyanya Gwandara a ƙaramar hukumar Karu ɗin sun ga ya dace ne su karrama basaraken, Alhaji Isa Kogi da sarautar bayan sun yi la’akari da gagaruman gudumawa da ya daɗe yana bayarwa wajen haɗa kawunan duka ƙabilu daban-daban da ke yankin nasa ciki har da su Yarbawa.

Ya ƙara da cewa sarautar ta musamman ta al’adar su wato Oba-Teru da ke nufin shugaba nagari da ke jin koke-koken al’ummar sa a ko yaushe ba tare da la’akari da banbance-banbancen siyasa, ƙabila da kuma addini ba, ba kowa ake naɗa masa ba sai wanda ya cancanta kamar shi mai martaba sarkin bakin, inda ya buƙace shi ya cigaba da waɗannan kyawawan halayya da ayyukan hidima da yake yi wa al’ummar nasa don kwalliya ta biya kuɗin sabulu wato a cimma burin sarautar da aka naɗa ma shi.

Shima a nasa jawabin, mai martaba sarkin al’ummar Yarabawa da ke yankin Nyanya Gwandara ɗin wato mai suna Oba Samson Adebayo Okutepa shima bayan ya taya sabon Oba-Teru nasu ɗin murnar, ya kuma yaba wa halayen sa nagari inda ya jaddada cewa ba shakka a ƙarƙashin kulawarsa al’ummar su na Yarbawa da ke yankin sa suna zaman lafiya da zumunci da maƙotan su sauran ƙabilun daban-daban, sannan sukan ji tamkar suna garuruwan su ne na asali inda ya ƙara da cewa tabbas wanda aka naɗa wa sarautar ya cancanta.

Haka shi ma a nasa ɓangaren da yake tofa albarkacin bakinsa, mai martaba sarkin yankin Aso a nan Karu, Alhaji Uzairu Sama’ila ya yaba wa hangan nesa da al’ummar Yarbawan yankin suka yi na naɗa wa Isa Kogi sarautar inda ya kuma bayyana cewa sam bai yi mamakin karrawamar ga basaraken ba idan aka yi la’akari da ɗimbin ayyukan jin ƙai da sadaukarwa da kuma yin tafiya da kowa da Alhaji Isa Kogi ke yi a kullum.

Sauran manyan baƙi da suka yi jawabin godiya na musamman ɗaya bayan ɗaya ciki har da mai magana da yawun al’ummar Yarbawan duk sun tabbatar da kyawawan sheda da duka waɗanda suka yi jawabi a baya suka faɗa akan sabon Oba-Teru ɗin inda ƙarshe suma suka buƙace shi ya ƙara himma ta wannan namijin ƙoƙarin.

Daga bisani da yake bayyanin godiyar sa, sabon Oba-Teru na al’ummar Yarbawa na Nyanya Gwandaran, Alhaji Isa Kogi wanda bayan kasancewar sa sarkin duka baƙin Masaka yana kuma riƙe da sarautar Matawallen Jankanwa da sarkin Gabas na Aso a Maraba da sauran su, ya jinjina wa al’ummar Yarbawan ɗin dangane da karrawamar da suka yi masa inda ya kuma gode wa duka ‘yan uwa da abokan arziki da ‘ya’yan sa da sauran takwarorin sa sarakunan gargajiya da suka hallara don taya shi murnar abin arzikin tare da yin alƙawarin cigaba da yin duka mai yiyuwa don agaza wa bil’adama baki ɗaya cikin ikon Allah kuma daidai gwargwado, kamar yadda ya kuma kira ga duka al’ummomi daban-daban a yankin su cigaba da son juna su kuma zauna lafiya da junansu a ko yaushe.

A ƙarshe, wakilin Blueprint Manhaja a jihar ya kuma ruwaito cewa, abubuwa da aka gudanar a yayin bikin wankan sarautar mai ɗimbin tarihi sun haɗa da karanto takaitaccen tarihin sarkin baƙin, Alhaji Isa Kogi da naɗin sarautar a hukumance da ɗaukan hotuna da sauran su inda su kuma a nasu ɓangaren mawaƙa da maroƙa suka nishaɗantar da ɗimbin mahalarta taron.

By ukarofi