Iran ta farmaki yankin ma’ajiyar nukiliyar Isra’ila

Spread the love

Harin makami mai linzami da Iran ta kai a garin Dimona da ke kudancin Isra’ila ya janyo firgici da tashin hankali a yankin, musamman ganin cewa wasu daga cikin hare-haren sun faɗa kan wata muhimmiyar cibiyar nukiliya.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu makaman sun tsallake kariyar iska ta Isra’ila, inda suka haddasa fashewa da lalacewar gine-gine tare da jikkatar mutane da dama, lamarin da ya nuna yadda rikicin ke kara tsananta, duk da matakan tsaro da ake dauka.

Harin ya biyo bayan jerin hare-haren ramuwar gayya tsakanin Iran da Isra’ila, inda kowanne bangare ke kokarin nuna karfin soji.

Masana sun bayyana cewa wannan rikici na iya janyo babbar barazana ga zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya, musamman idan aka ci gaba da kai farmaki kan muhimman wurare kamar cibiyoyin makamashin nukiliya da sansanonin soja.

By Babaji