Samun kaina a Kannywood ce babbar nasarar da na samu – Rahina Bello

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A wannan mako filin Nishaɗi ya zanta da wata matashiya ‘yar fim da ta shiga harkokin finafinai da ƙafar dama, Rahina M. Bello, wata matashiya ce da cikin ƙanƙanin lokaci ta yi fina-finai da yawa, a zantawarta da wakilinmu a Kano, za ku ji yadda a cikin shekara guda (Heena) ta shirya finafinai goma. Ku biyo mu:

MANHAJA: Za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatunmu?
Rahina: Sunana Rahina M. Bello amma an fi sanina da Heena.

Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?
An haifeni a barikin Sojoji na Ibadan, babana Soja ne, amma yanzu ina wajen kakannina ɓangaren mahaifiyata, kuma na kammala sakandare a shekarar 2021, kuma ina da burin na ci gaba da karatu a shekara mai zuwa.

Ta yaya kika samu kanki a masana’antar fum ta Kannywood?
To Ni dai na shiga harkar fim ne ta hannun Darakta kuma actor Mas’ud Umar Gwammaja, wanda aka fi sani da MM Sidi. Na same shi na nuna masa sha’awata ta shiga harkar fim, abinda ya fara yi min magana shi ne iyayena sun yarda? Sai na je na tambayi iyayena suka kuma amince, bayan ya samu tabbaci daga mahaifana sannan sai ya ce idan zai yi aiki na rinqa zuwa ina kallon yadda ake yi, to ka ji yadda aka yi na shiga fim.

Da wane fim kika fara?
Na fara harkar fim a December 2021, shekara guda kenan, kuma na fara da wani fim ne mai suna ‘Ƙabilanci’ fim ne mai dogon zango.

Daga shigarki zuwa yanzu fim nawa ki ka yi?
Na yi finafinai goma amma ba zan iya kawo sunayensu dukka ba, amma akwai ‘Ƙabilanci’, ‘Marainiya’, ‘Rumfar Maishayi’ da sauransu.

Daga lokacin da kika shiga harkar fim zuwa yanzu wane irin ƙalubale za ki iya cewa kin samu?
Gaskiya zan iya cewa ban samu kowanne irin ƙalubale ba, duk da yake ban daɗe ba a Kannywood, amma nasan ba za a rasa ƙalubale ba, ko da anan gaba ne, fatana Allah ya kawo mana jarrabawa mai sauƙi da za mu iya ɗauka.

Waɗanne irin nasarori za ki iya cewa kin samu?
Daga cikin nasarorin da na samu shi ne na samun kaina a cikin masana’antar Kannywood, wannan babbar nasara ce a gare ni, kuma ina zaune da kowa lafiya duk inda na je aiki muna rabuwa lafiya da kowa. Duk da yake kafin na shiga a na ta faɗin abubuwa mara sa daɗi akan ƴan fim, amma da na shiga banga komai da ake faɗa ba. domin idan wani ko wata ta yi laifi a Kannywood wanda ya yi laifin ya kamata a yi wa magana, ya gyara amma ba ayi jam’i ba. Kowacce sana’a tana da mutane kirki kuma ta na da ɓatagari.

Mene ne burinki a Masana’artar Kannywood?
Burina shi ne, na zama jaruma fitacciya, ta yadda duk inda na shiga mutane za su so su ganni kuma su yaba da ni.

Rahina

Ya batun aure fa?
(Dariya) Ina samun mijin aure wanda na yaba da hankalinsa da tarbiyyarsa da nutsuwarsa, shi ma ya yarda da nawa; to zan yi aure.

Ko yanzu idan miji mai waɗannan abubuwan kika lissafa ya fito za ki ajiye fim ki yi auren?
A’a a yanzu gaskiya idan miji ya fito ba zan yi aure ba, saboda ina da burin yin karatu na zama likita kafin na yi aure, amma idan na samu wanda muka daidaita sai na ƙarasa karatu a gidan mijina, domin gaskiya ina son karatu.

Mene ne fatanki ga masoyanki?
Ina yi masu fatan alheri da kuma fatan Allah ya haɗa kawunanmu Ya kaɗe fitina.

Mun gode.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *