Maikatanga ya samu kambun karramawa a matsayin ƙwararren mai ɗaukar hoto a gasar ‘GLF Africa 2022’

Daga AISHA ASAS a Abuja

Ƙwararren ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Malam Muhammad Sani Maikatanga, ya yi nasarar lashe kambun ƙwararren mai ɗaukar hoto a gasar da Cibiyar Masu Kula da Hoton Ƙasashen Duniya (GLF) ta gudanar ta wannan shekara.

Maikatanga ya samu wannan nasarar ne da hotonsa da ya yi wa laƙabi da ‘Fishers on the Run’, wanda ya ɗauka a bikin al’ada na kamun kifi da ake gudanarwa duk shekara a garin Argungu da ƙarƙashin Jihar Kebbi.

Hoton ya samu ƙuri’u masu tarin yawa da suka yi wa saura zarra, wanda hakan ne ya kai shi ga taka matakin nasara a wannan gasar.

Global Landscapes Forum GLF ƙungiya ce da ke kula da kusurwowin duniya da kula da hotunan da suka fito daga cikin su. Babbar ƙungiya ce a duniya da take ilimintarwa kan muradun ƙarni da yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris.

Ɗaya daga cikin ayyukan Sani Maikatanga

Ƙungiyar na ƙoƙarin ganin ta inganta muradun Majalisar Ɗinkin Duniya 17, daga cikin su akwai samar da aiki ga matasa, abinci, saisaita bambancin jinsi da kuma samun mafita a sauyin yanayi.

Ita wannan ƙungiyar na da haɗin gwiwa da manyan ma’aikatu masu zaman kansu na duniya, kamar irin su, Majalisar Ɗinkin Duniya ɓangaren da ke kula da muhalli UNEP, Babbar ma’aikata mai bada tallafi ta Ƙasar Jamus JIZ, Babbar ma’aikata mai kula da kiyon dabbobi IINBAR, sai CIMOD, IFOAM, Bankin Duniya da sauransu.

A vangare ɗaya, ƙungiyar na samun tallafi daga wasu sanannun ƙungiyoyi da ma’aikatu da suka haɗa da; BMUB, BMZ, FOLUR, THEGEF da kuma wasu daga cikin hukumomin gwamnati.