Sanannen ɗan kasuwan nan, kuma Sanata Ifeanyi Ubah ya gamu da mutuwar fuju’a a wani otel da ke Landon
Ubah ya gamu da ajali ne bayan ta bayyana cewa yana da ciwon zuciya kuma ya mutu jiya a Landan. Ya kasance mai shekaru 52.
Wasu ‘yan uwa da suka haɗa da matar shi, sun fara zaman makoki bayan da aka samu labarin cewa ɗan uwan nasu ya mutu a wani otel da ke babban birnin kasar Birtaniya, jaridar The Gazette ta ruwaito jim kaɗan bayan da Sahara Reporters ta fara yaɗa labarin a safiyar ranar Asabar.
Mista Ubah ya kasance shugaban kamfanin mai na Capital Oil na tsawon shekaru.
A shekarar 2014, Mista Ubah ya tsaya takarar gwamnan Anambra a karkashin jam’iyyar Labour amma ya sha kaye. Daga nan ya koma jam’iyyar Young Progressive Party (YPP), inda ya lashe kujerar Sanata a 2019 da 2023.
Daga baya a shekarar 2023, Mista Ubah ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya kasance Sanata a Nijeriya har zuwa rasuwarsa.
