Ku bada ƙarfinku ga zaɓe maimakon zanga-zanga – Kwankwaso

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da laifuka shida na siyasa da tattali yayin da ya buƙaci al’ummar Nijeriya su mayar da hankali kan zaɓe ba zanga-zanga ba.

Kwankwaso ya faɗi haka a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya fitar game da batun zanga-zangar ‘EndBadGovernment’, yana mai nuna damuwa kan halin da Nijeriya ta tsinci kanta inda ya danganta hakan da gazawar gwamanti tun daga shekarar 2007.

Ya ce, shugabanci mai kyau da adalci na girmama dokar ƙasa, bayyanawa ga kowa, da kuma adalci ke sa a samu haɓakar tattalin arziƙi da kuma cigaban ƙasa, yana mai cewa rashin waɗannan ababe su suka haifar shiga halin ƙunci da ƙasar ta tsinci kanta a ciki.

Sanata Kwankwaso ya ce, laifuka shida da su ka faru a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu sun haɗa da; shiga lamuran sarautar Kano, tsige Mataimankin gwamnan Jihar Edo, samuwar rikicin siyasa a Jihar Ribas, shirya maƙarƙashiya wa matatar Aliko Ɗangote, cecekuce kan yarjejeniyar Samoa, da kuma rikici tsakanin Sanata Ali Ndume da shugabancin jam’iyyar APC. Sai yaɗuwar rashin tsaro a cikin al’umma da laifukan sata.

Ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su kasance masu haƙuri da bai wa gwamnati goyon baya don a cimma nasara, amma su kayar da su a zaɓe yayin da su ka gaza sauke nauyin da ke kan su.

Bugu da ƙari, ya yi tsokaci game da batun zanga-zangar tsadar rayuwa, yana mai gargaɗin yiwuwar aukuwar tashin-tashina da hargitsi inda ya ce a madadin haka, su sauya fushinsu zuwa tunanin yadda za a fita daga halin da ake ciki ta hanyar sauya gwamanti a lokacin zaɓe.

By Babaji