Sanata ya raba taki har da ‘yan adawa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin shirinsa na samar da taki don sauƙaƙa wa manoma raɗaɗin wahalar noma, Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar mazaɓar gundumar Kebbi ta Arewa ya raba takin zamani a mazaɓarsa.

Da ya ke jawabi jiya Alhamis a wajen ƙaddamar da rabon takin, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kebbi Alhaji Usman Bello Suru ya bayyana cewa Sanata Yahaya Abubakar Mallamawan Kabi ya umarci a bai wa kowa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba saboda wakilcin da ya ke yi ba na al’ummar PDP kaɗai ba ne.

Haka zalika yana da tabbacin ba ‘ya’yan jam’iyyar PDP kaɗai suka zaɓe shi ba saboda haka a wajensa kowa yana da haƙƙin da ya kamata ya ci moriyar daga wajensa.

Alhaji Nasiru Nasco Ɗakingari ɗaya daga cikin shugabannin matasa daga ƙaramar hukumar mulki ta Suru ya yaba wa Sanata Yahaya Abubakar, inda ya ce a tarihin siyasa ba su tana ganin irin haka ba saboda a tarihin siyasa ɗan adawa tamakar maƙiyi ne wanda ba a nufinsa da kowane irin samu amma sai ga shi wannan Sanatan ya fito fili ƙarara ya bayyana cewa dole ne a bai wa kowa ba ruwansa da wani ɗan jam’iyyarsa ko ɗan wata jam’iyya.

“Fatan mu da Allah ya saka masa da alheri ya biya buƙatunsa,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga ‘yan siysa da su yi koyi da Sanata Yahaya Abubakar Mallamawan Kabi wanda ba shakka yin koyi da shi wata turba ce ta wanzar da zaman lafiya tsakanin al’umma.

An dai raba takin a matakin ƙananan hukumomi inda bayar da ton talatin a Argungu, Augie, Arewa, Dandi, Suru da kuma Bagudo.

Haka zalika ita ma jam’iyyar adawa ta APC ta samu ton talatin.

Bikin dai ya samu halartar manyan ‘yan siysa daga gundumar mazaɓar Kebbi ta Arewa da kuma waɗansu sassa daga cikin jihar Kebbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *