Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya rantsar da sabbin kwamishinoninsa 20 tare da ma’aikatunsu daban-daban, inda ya umurce su da bin ƙa’idar aikin.
Bikin rantsarwar ya gudana ne a babban ɗakin taron da ke gidan gwamnatin jihar a Damaturu.
Gwamna Buni ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe tare da Mambobinsa bisa gaggauta tantance sunayen kwamishinonin, ya ce hakan ya nuna kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin ɓangaren zartaswa da na majalisa don kawo ci gaban al’ummar jihar Yobe.
Haka kuma, Gwamnan ya taya sabbin kwamishinonin murna bisa naɗa su Kwamishinoni kuma mambobin Majalisar Zartarwar jihar.
Ya ce ko shakka babu, suna sane da aikin da yake gabansu, tare da buƙatar jan ɗamarar kawo sauyi mai ma’ana wajen ci gaban al’ummar jihar, tare da azama wajen aiwatar da tsare-tsare da tsare-tsare masu ra’ayin jama’a don ci gaban jihar.
“An zaɓe ku ne domin yin hidima ga al’ummar jiharmu mai albarka. Saboda haka ya kamata ku zage dantse don yin shugabanci nagari tare da gaskata amincin da jama’a suka ba ku a cikin aminci, himma, sadaukarwa don ci gaban Yobe da al’ummar ta.”
Gwamna Buni ya kara da cewa, “A yayin da muke ci gaba da wa’adinmu na biyu kuma na ƙarshe, dole mu himmatu matuƙa wajen cimma burin da muka sa a gaba da kuma biyan buƙatun jama’armu. Wannan wani aiki ne wanda dole ne mu cimma hakan domin ‘ya’ya da jikokinmu masu zuwa su yi alfahari da mu.”
Sabbin kwamishinonin da aka rantsar sun haɗa: da Alh. Aji Yerima Bularafa – Ma’aikatar Ƙirkiro Hanyoyin Bunƙasa Arziki da Samar da ayyukan yi, Ali Mustapha Goniri – Ma’aikatar Ayyukan Gona, sai Hajiya Ya Jalo Badama – Ma’aikatar Harkokin Mata, Hon. Musa Mustapha – Ma’aikatar Sufuri da Makamashi, Ahmed Buba Abba Kyari – Ma’aikatar Gidaje, Engr. Usman Ahmed – Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Mohammed Abatcha Gaidam – Ma’aikatar Kuɗi, Hon. Kaigama Umar Yunusari – Ma’aikatar Kasuwanci, Alh. Ibrahim Adamu Jajere – Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu.
Sauran su ne Hon. Yusuf Umar Potiskum – Ma’aikatar Harkokin Addinai, Barr. Saleh Samanja – Ma’aikatar Shari’a kuma Antony Janaral, Prof. Mohammed Bello Kawuwa – Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Engr. Umar Wakil Dudaye – Ma’aikatar Ayyuka sai Hon. Abdullahi Bego – Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Al’adu da Harkokin Yau da Kullum.
Sai Dr. Mairo Amshi – Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai da tallafi, Hon. Mohammed Gagiyo – Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, Dr. Mohammed Lawan Gana – Ma’aikatar Lafiya, Yakubu Karasuwa – Ma’aikatar muhalli, Dr. Mohammed Sani Idriss – Ma’aikatar Ilimi a Matakin Farko da Sakandire yayin da Barma Shettima zai kula da Ma’aikatar Matasa da Wasanni.