Sanata Yahaya ya raba kaya a makarantun sakandare a mazaɓarsa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin shirinsa na tallafa wa ɓangaren ilmi, Sanata mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi ya raba kaya a makarantun sakandare huɗu da ke mazabarsa da suka haɗa da makarantar maza ta Kanta Unity College Argungu da makarantun mata na Augie, Argungu da kuma Ɗakingari.

Kayan dai sun haɗa da katifu 396, zannuwan gado 396 da filallu 396, inda kowace makaranta ta samu 99 daga cikin kayan, sauran sun haɗa da manyan tukwanen girki 60 cokula farantin cin abinci dozin ashirin-ashirin, kofuna da kujeru da tebura na roba biyar-biyar.

Da ya ke jawabi a makarantar ‘yan mata ta da ke garin Ɗakingari Alhaji Musa Wazirin Tiggi a madadin Sanata Yahaya, ya bayyana cewa wakilcin Sanata Yahaya ba na ɗumama kujera ba ne a zauren majalisa, ya je ne don ya isar da buƙatun al’ummar mazaɓarsa, kuma ba shakka ya isar da saƙo saboda duk faɗin mazavar gundumar Kebbi ta arewa babu wata mazaɓa wacce ba ta ci wata moriyar wakilcin sa ba, saboda haka yanzu ya rage wa al’ummar mazaɓarsa da biya shi bashi don yanzu shi ne ke bin bashi. Wanda in sha Allahu ba da daɗewa ba za mu zo da buƙata.

Jami’in gudanarwa a ƙaramar hukumar mulki ta Suru Alhaji Alhaji Nasir Nasco Ɗakingari ya bayyana cewa wannan somintaɓi ne, saboda duk da ya ke akwai buƙatu da yawa a kowane ɓangare amma dai in sha Allahu ba wani sashe da aka mayar saniyar ware a wakilcin Sanata Dokta Yahaya.