Sanatoci sun fatattaki sanatan da bai taɓa halartar zaman majalisa ba

’Yan majalisar Japan sun kori wani sanata daga Majalisar Dattawan ƙasar bayan ya kwashe wata bakwai bai halarci zaman majalisar ba.

Sanatan, wanda fitacccen mai amfani da shafin YouTube ne, ya zama ɗan majalisa na farko da aka kora ba tare da ya tava shiga zauren Majalisar Dattawan ba tun da aka zaɓe shi.

Sanatocin sun kori Sanata Yoshikazu Higashitani ne a ranar Talata sakamakon rashin halartar zaman majalisar.

Tunda aka zaɓe shi wata bakwai da suka gabata, ko sau daya bai taɓa halartar zaman majalisar ba.

Kwamitin Ladabtarwa na majalisar ne ya yanke hukunci korarsa saboda ci gaba da ƙin halartar zaman majalisar da yake yi.

A watan Yulin bara aka zaɓi Higashitani a majalisar, kuma sanatan, wanda aka fi sani da ‘GaaSyy’ a shafin YouTube ya yi fice wajen wallafa shahararrun bidiyoyinsa, ya zama sanata na farko da aka taɓa kora bisa laifin ƙin halartar majalisa.

Hukuncin kora shi ne hukunci mafi tsauri da ɗan majalisa zai fuskanta. Kuma a tarihin ƙasar wannan ne karo na biyu da hakan ta taɓa faruwa tun 1950.

Nan gaba kaɗan ne a makon nan majalisar za ta tabbatar da korar sanatan a hukumance.

Rahotonni sun ce sanatan na zaune ne a kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Kafofin yaɗa labaran Japan sun ce sanatan ya ki halartar zaman majalisar ce sakamakon fargabar kama shi bisa zargin aikata laifin zamba da bata suna da wasu shahararrun mutane ke yi masa.

Yana ɗaya daga cikin zavavvun ’yan majalisa biyu daga jam’iyyar hamayya ta NHK, jam’iyya ɗaya tilo da ke kiraye-kirayen sauya ɓangaren yaɗa labaran ƙasar.

Jaridar Asahi Shimbun ta ce jam’iyyar na yawan sauya sunanta saboda dalilai na neman shahara.

A makon jiya, Majalisar Dattawan ta nemi Higashitani ya je birnin Tokyo domin neman afuwa a zauren majalisar kan kin halartar zaman majalisar da ya yi.

’Yan majalisar sun ce wannan ita ce dama ta ƙarshe da za su bai wa sanatan domin ci gaba da kasancewa mamba a majalisar.

Sai dai Higashitani ya qi yarda ya halarci zaman majalisar, kamar yadda abokan aikinsa suka buƙata.

Maimakon haka, sai ya bayyana a shafinsa na YouTube cewa zai tafi ƙasar Turkiyya.

Kuma ya ce, yana shirin sadaukar da albashinsa domin tallafa wa mutanen da bala’in girgizar ƙasar Turkiyya ta shafa.

Rashin halartarsa zaman majalisar ya tunzura sanatocin, waɗanda suka amince da kaɗa ƙuri’ar korarsa a wannan mako.

Ɗan majalisa ɗaya tilo da ke jam’iyya ɗaya da sanatan, Hamada Satoshi, ya ce korar sanatan da aka yi bisa laifin rashin halartar majalisar ba ya kan tsarin doka.