Mahajjatan Umarah 20 sun rasu, 29 sun jikkata a hatsarin mota a Makka

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga ƙasar Saudiyya sun ce, wasu mahajjatan Umarah su 20 sun riga mu gidan gaskiya, sannan 29 jikkata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a Makka.

Bayanai sun ce mahajjatan sun gamu da wannan jarrawar ce a kan hanyarsu ta zuwa aikin Umara a Makka a ranar Litinin.

Wata majiya ta ce mai yiwuwa adadin waɗanda suka rasa ransu ya ƙaru duba da yanayin raunukan da wasunsu suka ji.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da ‘yan asalin Saudiyya da kuma baƙi daga sauran sassan duniya da suka tafi Saudiyya don yin Umarah.

An ce hatsarin ya auku ne a hanyar Aqabat Shaar bayan da motar da ke ɗauke da su ta baro Khamis Mushait zuwa Abha.

Ana kyautata zato shamyewar burki ne ya haddasa hatsarin inda motar ta daki gefen a gindin wani tsauni.

Aukuwar hatsarin ya haifar da rufe hanyoyin zuwa Aqabat Shaar don bai wa jami’an ba da agaji damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Manhaja ta kalato cewar an kwashi waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci don yi musu magani.

Hatsarin na zuwa ne a cikin watan Ramadan, watan da Musulmi daga sassan duniya kan ziyarci Makka don ibadar Umarah.