Mai shekara 85 ya auri mata ta 11

Wani dattijo mai shekara 85 ɗan ƙasar Saudiyya mai kuma sha’awar aure-aure da tara ’ya’ya, ya sake ɗaura aure da wata matar a karo na 11 domin ya cike gurbin ta huɗu.

Mutumin mai suna Ali Al Balawi ɗan ƙasar Saudiyya ya sake ƙara auren ne a karo na 11 da wata mace ’yar ƙasar da ba a bayyana sunanta ba.

An ɗaura auren ne a garin Tabbuka da ke Arewa maso Yammacin ƙasar.

Ali na da mata uku da kuma ’ya’ya 38, wanda suka ƙunshi maza 18 da mata 20 da kuma jikoki 88, ya kuma ƙara auren ne a karo na 11 a cikin lissafin matan da ya aura kawo yanzu.

An yi walimar auren a garin nasu wanda ya samu halartar ’yan uwa da abokai da kuma dangi.

An rawaito dattijon na cewa, yana da ƙoshin lafiya bai kuma taɓa gamuwa da wata larurar rashin lafiya ba inda ya ce, “don haka ni babu abin da zai hana ni ƙarin aure”.

Bugu da ƙari, Ali ya kuma ce, yana da yalwar aljihu, sannan kuma Allah Ya wadata shi da lafiyar jiki da kwakwalwar da zai ɗauki nauyi da kuma kula da mata huɗu da kuma ɗawainiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *