Sarkin Katsina ya halarci sallar idi a masallacin Ƙofar Guga

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, ya gudanar da sallar udi tare da dubban al’ummar Musulmi wajen gudanar da sallar udi ta babbar sallah a masallacin udi na Ƙofar Guga da ke birnin Katsina.

Masallacin ya cika maƙil da masu ibada daga sassa daban-daban na jihar da suka halarci sallar domin gudanar da wannan babbar ibada ta babbar sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.

Bayan gudanar da raka’o’in sallar udi, an gabatar da huduba inda malamai suka yi bayani kan muhimmancin babbar sallah da kuma darussan da ke tattare da ibadar layya kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

A cikin hudubar, an jaddada muhimmancin yin layya ga waɗanda Allah ya ba iko, tare da bayyana cewa layya na daga cikin manyan sunnonin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da ke nuna biyayya da kusanci ga Allah maɗaukakin sarki.

Malaman sun bayyana cewa a maimakon wasu mutane su karkata wajen sayen raguna domin nuna kawaici ko aji kawai ba tare da yin layya ba, ya kamata Musulmi su fifita aiwatar da ibadar layya saboda irin girman lada da falalar da take da ita a Musulunci.

Huɗubar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da taimakon juna, kula da mabuƙata da kuma tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin jama’a musamman a irin wannan lokaci na bukukuwa.

An gudanar da taron sallar cikin tsaro da kwanciyar hankali, yayin da jama’a suka nuna farin ciki tare da saƙonnin barka da sallah bayan kammala ibadar.

By ukarofi