Sarkin Katsina zai naɗa Abdullahi Aliyu a matsayin Dujuman Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Nan da makwanni uku mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman zai naɗa shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majilisar wakilai Abdullahi Aliyu sarautar Duhuman Katsina.

Bayanin haka kuwa ya fito ne a wata takarda dauke da sa hannun mataimakin na musamman a harkokin yaɗa labarai na ɗan majalisar Frances Sardaunan.

Me Frances ya bayyana cewa jajircewar ɗan majalisar wajan bunƙasa tattalin arziki tare da tallafawa al’ummar mazaɓarsa yasa Sarkin Katsina zai karrama shi da wannan sarauta.

Ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazabar musawa da matazu a Majilisar wakilai yayi karatun digiri nasa akan kimiyyar siyasa da tattalin arzikin ƙasa a jami’ar Bayero ta Kano.

Ya riƙe muƙamin daban daban a ciki harda mataimakin na musamman a ƙarƙashin tsohon gwamna Aminu Bello Masari a lokacin da kuma Mallam Dikko Radda kafin Dikkon ya zama gwamnan Katsina.

Mataimakin na musamman ya kara da cewa ana sa ran za’a gudanar da ƙwarya ƙwaryar durba watau Hawzan Dawaki na alfarma .

Gwamnoni da ministoci tare da yan Majilisar ƙasa sun nuna sha’awar su ta halartar bukin naɗin sarautar da da za’a yi a fadan mai martaba sarkin Katsina.

By ukarofi