Saudiyya ta ɗage haramcin zirga-zirgar jiragen saman Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masarautar Saudiyya ta ɗage dakatar da zirga-zirgar jiragen saman Nijeriya a ƙasarta watanni uku bayan da ta sanya dokar hana fita sakamakon ɓullar cutar Korona.

Sanarwar da ta ɗage haramcin an ba da ta ne a ranar Asabar inda Masarautar ta kuma cire takunkumin annobar Korona da yawa ta yadda za ta ba da damar aikin Hajji na 2022.

A cewar sanarwar da aka gani a shafin Twitter na Saudi Gazette, Masarautar ta kuma ɗage dakatar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye da shigowa daga wasu ƙasashe 17.

Waɗannan sun haɗa da Afirka ta Kudu, Namibiya, Botswana, Zimbabwe, Lesotho, Eswatini, Mozambique, Malawi, Mauritius, Zambia, Madagascar, Mauritius, Zambia, Madagascar, Angola, Seychelles, Congo, da sauransu.

Idan dai ba a manta ba Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (GACA) a ƙasar Saudiyya ta tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Nijeriya a wata takarda da ta fitar ga dukkan kamfanonin jiragen sama da ke aiki a Saudiyya a ranar 8 ga watan Disamba.

Bayan dakatarwar da kamfanin na Azman Air, kamfanin jiragen Nijeriya ɗaya tilo da ke zuwa Saudiyya ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama, wanda hakan ya dakatar da dukkan shirye-shiryen aikin Umrah a watan Disambar bara.