Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya ce sabon sauye-sauyen da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi ya ceto Nijeriya daga halin ƙunci.
Soludo wanda tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) ne ya ce duk da cewa yana sukar Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya, IMF, amma rawar da suka taka a waɗannan sauye-sauye abin a yaba ne.
“Dole ne mu yaba da cewa mun yi nisa tare da amincewa da cewa akwai sauran rina a kaba, kuma dole na faɗi cewa sauye-sauyen da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi a halin yanzu sun kai tattalin arzikin ƙasar tudun-mun-tsira.
“Ayyukan da Bankin Duniya, IMF, London Financial Times, da hukumomin tantancewa irin su Fitch da Moody’s, a ganina, abin a yaba ne. Mutane da yawa sun san cewa ina sukar IMF da Bankin Duniya, a matsayina na Gwamnan Anambra har ma na ƙi amincewa da lamuni na Bankin Duniya saboda sharuɗɗansa. Duk da haka, a game da yanayin sake fasalin tattalin arziki da sauran su, Babban Bankin Duniya ya taka muhimmiyar rawa.
Ya ci gaba da cewa, “A shekarar 2023, na kwatanta halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki a matsayin “mataccen doki”, kuma jama’a na dad da shiga cikin halin “ha’ula’i”, gami da yuwuwar sallamar ma’aikata da kuma tarin basussukan fansho.”
“Gwamnatin da ta shuɗe ta zartar da wani ƙuduri a 2023, ta ce tallafin zai ƙare a ƙarshen watan Yuni. Hakan ya nuna mun kai ƙarshe,” inji Soludo.
Gwamnan ya sake duba yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta bi “hannu da hannu” yayin da ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ci gaba da tafiya
