SERAP ta yi martani kan hukuncin kotu a shari’ar zargin ɓata suna wa DSS, ta bayyana mataki na gaba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, ta yanke, inda ta umarci ƙungiyar ta biya diyyar ɓata suna ga wasu jami’an Hukumar Tsaro ta DSS.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu, a hukuncin da ya yanke a ranar Talata, ya bayar da umarnin SERAP ta biya tarar Naira miliyan 100 ga jami’an DSS biyu, Sarah John da Gabriel Ogundele.

Kotun ta kuma umarci SERAP da ta fitar da afuwar jama’a, ta biya Naira miliyan 1 a matsayin kuɗin shari’a, tare da ƙarin kashi 10 cikin 100 na ruwa duk shekara kan kuɗin har sai an kammala biya.

A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan ta, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu, SERAP ta ce ba ta amince da hukuncin ba, kuma ta bai wa manyan lauyoyinta, Tayo Oyetibo, SAN, da Ebun-Olu Adegboruwa, SAN, umarnin daukaka ƙara.

ƙungiyar ta bayyana hukuncin a matsayin “babban koma baya ga ‘yancin faɗar albarkacin baki da sararin aiki na ƙungiyoyin farar hula,” tana mai cewa shari’ar na ɗaga tambayoyi masu zurfi kan yadda ake amfani da dokar bata suna a lokutan da ake sukar hukumomin gwamnati.

SERAP ta ce wallafar da ta yi a ranar 9 ga Satumba, 2024, game da DSS, an yi ta ne bisa muradin jama’a, bayan wani lamari da ya faru a ofishinta da ke Abuja, inda jami’an DSS suka kai ziyara bayan ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya binciki zargin cin hanci a NNPCL tare da duba ƙarin farashin man fetur.

A cewar SERAP, jami’an tsaron da suka kai ofishinta sun nemi takardu da suka shafi rajista da ayyukan ƙungiyar, yayin da ma’aikata suka ji tsoro da fargaba sakamakon yadda jami’an tsaro da motocinsu suka kewaye wurin.

ƙungiyar ta kuma jaddada cewa wallafar da ake ƙorafi a kanta ba ta ambaci sunayen jami’an DSS da suka shigar da ƙara ba, don haka ba za a iya cewa ta bata musu suna kai tsaye ba.

SERAP ta kuma yi nuni da cewa kalaman nata suna ƙarƙashin kariyar kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokokin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa da ke ba da ‘yancin faɗar albarkacin baki.

ƙungiyar ta nuna damuwa kan tasirin wannan hukunci ga ƙungiyoyin farar hula da masu fafutukar yaki da cin hanci, tana mai cewa yanzu haka kotun ɗaukaka ƙara ce za ta yanke hukunci kan batutuwan da suka taso a shari’ar.

Shari’ar mai lamba FCT/HC/CV/4547/24, jami’an DSS biyu, Sarah John da Gabriel Ogundele, ne suka shigar kan wani rubutu da SERAP ta wallafa a kafafen sada zumunta, inda ta zargi jami’an da cin zarafi da kuma mamaye ofishinta ba bisa ka’ida ba.

A nasa martanin, ɗaya daga cikin lauyoyin SERAP, Ebun-Olu Adegboruwa, SAN, ya ce hukuncin bai yi daidai da hujjojin doka da aka gabatar a kotu ba, musamman kan batun matsayin DSS a doka, ko DSS ce ko SSS.

Ya kuma ce kotun ba ta yi la’akari da muhimmin batu ba, wato ko jami’an gwamnati na iya kai ƙarar bata suna a madadin hukumominsu dangane da abin da ya faru yayin gudanar da aikinsu.

Adegboruwa ya ƙara da cewa duk da cewa masu ƙara sun ce har yanzu ana binciken su a wurin aikinsu kan abin da ya faru a ofishin SERAP, kotun ta yanke hukunci kan SERAP ba tare da cikakkiyar shaida kan waɗanda aka bata wa suna ba.

Ya soki yadda aka bayar da diyyar Naira miliyan 100, yana mai cewa ya kamata a yi la’akari da matsayi da albashin masu ƙara, waɗanda bai bayyana a kotu ba.

Haka kuma ya ce akwai ruɗani a shari’ar, domin masu ƙarar sun je aiki ne da kuɗin gwamnati amma suna neman diyya ta kashin kansu daga abin da ya shafi aikin gwamnati.

Ya kuma soki yadda kotun ta bayar da kashi 10 cikin 100 na ruwa kan kuɗin, alhali ba shari’ar kwangila ba ce, kuma ba a gabatar da hujjar hakan ba.

A cewarsa, wannan hukunci ba shi da misali a doka, kuma yana da haɗari ga dimokuraɗiyya, domin ana iya amfani da shi wajen toshe bakin ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Ya tabbatar da cewa za su ɗauki matakin daukaka ƙara nan take.

By ukarofi