Daga AMINA YUSUF ALI
A yammacin ranar Litinin ɗin da ta gabata ne, al’ummar Najeriya da wasu wuraren suka tsinci kansu a halin ɗaukewar shafukan fesbuk da wasaf da instagiram ɗif! Har na tsawon awanni. Al’amarin ya faru ne tun daga ƙarfe biyar na yammacin ranar Litinin din. Inda al’umma suka kasa sarrafa shafukan a tsakanin waɗancan lokutan.
Bincike ya nuna cewa, wannan al’amari da ya faru, ya jawo wa mawallafin shafukan, Mark Zuckerberg ya tafka mummunar asara har ta Dalar Amurka Biliyan Bakwai. Wannan asara da shi Zuckerberg ya tafka, ta komar da shi baya a matsayinsa na ɗaya daga jerin waɗanda suka fi kowa kuɗi a Duniya.
Inda ya mayar da shi matsayinsa a ƙarƙashin attajiri Bill Gate, duk da a baya matsayinsa ya fi na Bill Gate a jerin sunayen masu kuɗin.
Shafukan zumunta na fesbuk da wasaf sun ɗauke ɗif na tsawon awanni huɗu. Yayin da shi kuma shafin instagiram bai dawo a wancan lokacin ba.
Amma har zuwa sanda aka gama haɗa rahoton nan, ba a san musabbabin da ya janyo ɗaukewar shafukan ba. Amma matsalar ɗaukewar ta yanke alaƙar sadarwa tsakanin mutane da dama kuma ta sa su a cikin halin damuwa.
Sai dai wani mai magana da yawun kamfanin fesbuk ɗin, wato mataimakin shugaban kamfanin, Nick Clegg, ya gaya wa tashar talabijin ta CNN cewa, yana da matukar wahala a gane takamaimai matsalar.
Amma ana tsammanin matsalar ba ta fasahar ƙere-ƙere ce ba kaɗai.