Shari’ar Gwamnan Kano: Kotu ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Kano ta ayyana ranar Laraba ta wannan mako a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar da ke gabanta inda Jam’iyyar APC ke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gabata.

A ranar Litinin da ta gabata Kotun ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin cikin sanarwar da ta aike wa ɓangarorin da shari’ar ta shafa.

Sakataren lauyoyin NNPP, Barrister Bashir T/Wurzici, ya tabbatar wa Jaidar Daily Trust da hakan, yana mai cewa lallai an miƙa wa tawagar lauyoyi takardar sanarwa da yammacin Litinin.

“Muna farin cikin cewar ranar ta zo, kuma muna murnar saboda mun san za a kori ƙarar.

“Muna fata Kotun ta bi hanyar da shari’ar zaɓen shugaban ƙasa ta bi saboda ƙararrakin sun yi kama da juna,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kano, Shehu Maigari, ya ce, “muna sa ran samun nasara a hukuncin duba da hujjojin da muka gabatar wa kotun, muna da tabbacin mu za mu yi nasara.”