Shari’ar nasarar Tinubu: Lauyoyin Tinubu sun zargi Manhajar Amazon da haifar da matsalar da INEC ta samu da Rumbun IReV

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ta bakin lauyoyinsa, ya shaida wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa Rumbun Adana Bayanai a Yanar Gizo na Amazon, ba shi da garanti, ya na iya samun matsala.

Sai dai kuma wani ƙwararren injinijya na Amazon ya ƙaryata lauyoyin Tinubu ɗin.

AWS Incorporated a ƙarƙashin Amazon ne suka buɗe wa INEC Rumbun Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta IReV, a lokacin zaven 2023.

Atiku da Peter Obi duk sun ƙalubalaci ƙin watsa sakamakon zaɓe, wanda su ka ce ba a watsa a IReV ba, kamar yadda INEC ta yi alƙawarin za ta yi.

Jayayyar ta zo mako guda bayan Peter Obi ya yi wa kotu saukalen lodin takardun sakamakon zaɓe kwafe 18,000 daga IReV, da ya ce dishi-dishi su ke, ba su karantuwa.

Ɗan takarar Shugaban Qasa a zaven 2023 a qarqashin jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ci gaba da danƙara wa wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa tulin hujjojin da ya ke neman kafawa domin neman yin nasara a kotu.

A ci gaba da zaman ranar Alhamis, Peter Obi ya yi wa kotu saukalen lodin takardun sakamakon zaɓe kwafe 18,000 daga IReV, da ya ce dishi-dishi su ke, ba su karantuwa.

Wani ƙwararren masanin manhaja da laƙanin sirrin kwamfuta ne ya bayar da wannan shaida cewa shafukan 18,000 duk ba a iya ganin sakamakon zaɓen da ke cikin su, saboda shafukan duk garara-garara su ke.

Lauyan Peter Obi, Onyechi Ikpeazu ne ya gabatar da mai bayar da shaidar, mai suna Erik Uwadiagwu, wanda ya yi nazarin ‘data’ ɗin bayanan sakamakon da ke cikin Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe na IReV, na INEC.

Uwadiagwu, wanda Farfesa ne a darasin lissafi, a Jami’ar Nnamdi Azikwe, Awka, Jihar Anambra, ya bayyana a gaban kotun bisa gayyatar Obi, domin bayar da shaida.

Kafin ya fara bayani sai da ya yi rantsuwar kaffara da Kwansitushin, a matsayin babban mai bayar da shaida na Peter Obi.

Ya ce ya yi nazarin shafukan IReV 18,000 daga Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe, wanda hotunan kwafen sakamakon zaɓe ne INEC ke lodawa a ciki, daga Na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Zaɓe, wato BVAS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *