Shawarwari 4 na Ƙasar Sin za su taimaka wajen samar da sabon abun al’ajabi a Asiya da yankin Tekun Pasifik

Daga CMG HAUSA

Ranar 18 ga wata, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping na ƙasar Sin ya bayyana cikin jawabinsa a yayin ƙwarya-ƙwaryar taron shugabanni mambobin ƙungiyar haɗin kan tattalin arziki ta Asiya da yankin tekun Pasifik APEC karo na 29 cewa, yanzu duniya ta sake shiga muhimmin lokaci a tarihi.

Asiya da yankin tekun Pasifik suna ƙara taka muhimmiyar rawa, yayin da matsayinsu ya samu ingantuwa sosai.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda 4 kan yadda za a hada hannu wajen raya makomar bai ɗaya a Asiya da yankin tekun Pasifik a sabon halin da ake ciki, wato kiyaye adalci a duniya, a ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Asiya da yankin tekun Pasifik, da tsayawa kan bude kofa ga ƙetare da dunƙule dukkan bangarori, a ƙoƙarin raya Asiya da yankin tekun Pasifik mai wadata, da nacewa kan raya Asiya da yankin tekun Pasifik mai tsabta da kyan gani ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma tsayawa kan taimakawa juna a Asiya da yankin tekun Pasifik, waɗanda ke da makoma iri ɗaya.

Ruhin waɗannan shawarwari 4 sun yi daidai da shawarwari guda 6 da Xi Jinping ya ambato cikin rubutaccen jawabinsa a yayin taron shugabannin masana’antu da kasuwanci na ƙungiyar APEC a ranar 17 ga wata.

Dukkansu sun taƙaita fasahohin da aka samu wajen samar da abun al’ajabi na Asiya da yankin tekun Pasifik, sun kuma tsara manyan tsare-tsare kan halin da ake ciki yanzu.

Shawarwarin na da ma’ana mai zurfi kan haƙiƙanin halin da ake ciki.

Ba za a samu ci gaba ba, sai an samu zaman lafiya tukuna.

Kana kuma, ci gaba ya na ba da tabbaci wajen samun zaman lafiya.

A matsayinta na muhimmiyar mambar ƙungiyar APEC, ƙasar Sin ta samu ci gaba sakamakon kasancewa a Asiya da yankin tekun Pasifik, yayin da ta ba da nata gudummowa wajen raya Asiya da yankin tekun Pasifik.

Ya zuwa shekarar 2020, jimillar yawan cinikin da ke tsakanin Sin da mambobin ƙungiyar APEC ta kai dalar Amurka triliyan 2.87.

Kwanan baya, an samu nasarar gwajin layin dogon Jakarta-Bandung mai saurin tafiya.

An fara aiki da tasoshin dakon kaya a layin dogo tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Laos.

Kana an fara amfani da babban titin dake tsakanin Phnom Penh da tashar jiragen ruwa ta Sihanoukville a ƙasar Cambodiya.

Lalle ayyukan raya ababen more rayuwar jama’a ƙarƙashin inuwar shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, sun kyautata haɗewar sassa daban daban a Asiya da yankin tekun Pasifik.

Ƙasar Sin za ta ci gaba da ɗaukar haƙiƙanin matakai don nuna yadda take aza harsashi a Asiya da yankin tekun Pasifik, da raya yankin da kuma kawo alheri ga yankin.

Mai fassara: Tasallah Yuan