Peng Liyuan ta ziyarci ɗakin adana kayan tarihi na fasaha na birnin Ayutthaya na Thailand

Daga CMG HAUSA

A yau da safe, bisa gayyatar da uwargidan firaministan ƙasar Thailand Naraporn Chan-ocha ta yi mata, uwargidan shugaban ƙasar Sin Peng Liyuan, ta ziyarci dakin adana kayan tarihi na fasaha na birnin Ayutthaya tare da abokan zaman shugabanni da wakilai masu halartar taron karba-karba na shugabannin mambobin ƙungiyar haɗin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da yankin tekun Pasifik wato APEC karo na 29.

An kafa dakin adana kayan tarihi na fasahar ne bisa ra’ayin mahaifiyar sarkin ƙasar Thailand Sirikit Kitiyakara, don yada fasahohin hannu na gargajiya na ƙasar, da kuma taimakawa matalauta a yankunan karkara samun kuɗin shiga da kansu.

Peng Liyuan ta yaba wa wannan batu, inda ta ce lamarin ya yi kama da yadda ƙasar Sin take yaƙi da talauci a yankunan karkara masu fama da talauci na ƙasar.

Yayin da ta ga kayayyakin da yaran da suka bar makaranta, waɗanda samu horo a makarantar koyon fasahohin hannu ta gidan sarkin ƙasar suka samar, Peng Liyuan ta bayyana cewa, za ta sayi wasu kayayyakin don goyon bayan aikin taimakawa matalauta da gidan sarkin ƙasar Thailand ke gudanarwa.

Mai Fassara: Zainab