2023: Duk jihar da rikicin siyasa ya tashi laifin gwamnoni ne – Mathew Kukah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Limamin Ɗariƙar Cocin Katolika na Sakkwato, Mathew Kukah, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya cewa su ɗora laifin ɓarkewar rikice-rikicen siyasa a kan gwamnonin jihohi.

Ya ce akasari duk rikicin siyasar da ya tashi da wanda zai tashi kafin nan da zaɓen 2023, duk gwamnonin jihohi ne musabbabinsu.

Kukah ya yi wannan tsokaci a cikin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya yi da shi a ranar Talata.

Ya ce wasu gwamnonin jihohi ƙiri-ƙiri su na hana jam’iyyun siyasa yin amfani wuraren taruka mallakar jihohi, lamarin da faston ya ce hakan na haifar da rikicin siyasa a jihohi daban-daban.

Wannan bayani na Kukah ya zo kwanaki huɗu bayan Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari Kan Tsaro, Babagana Monguno ya bayyana cewa a cikin kwanaki 30 bayan fara kamfen, an samu tashe-tashen hankula a wurare 52 cikin jihohi 22.

“Ni ina ganin cewa gwamnoni sun fi sauran rukunan ‘yan Nijeriya laifin haddasa varkewar tashe-tashen hankula. Saboda su ne masu wuƙa da naman da ke riƙe da wasu wuraren da dalilin su rikicin ke yawan tashi,” inji Kukah.

Ya ce sannan kuma wasu gwamnonin da su ka canja sheƙa zuwa wata jam’iyyar na haddasa rikici ta hanyar ƙoƙarin tirsasa wa sauran jami’an gwamnati bin su zuwa jam’iyyar da su gwamnonin su ka koma.

“Kuma abin takaici ne yadda waɗannan gwamnoni ke nuna kamar ba su da masaniyar cewa magoya bayan su na kekketa fastar jam’iyyun adawa.”

Ya ce abin damuwa ne matuƙa yadda waɗannan gwamnoni ba su ɗaukar darasi daga kura-kuren da su ka tafka a baya, wanda ya yi sanadiyyar varkewar tarzomar siyasa.

Da ya ke bada misalin halayyar ‘yan siyasa da wani bidiyon da aka nuno Atiku Abubakar da Bola Tinubu zaune a filin jirgi su na raha da annashuwa, Kukah ya ce hakan darasi ne da ya kamata talaka ya ɗauka cewa su fa ‘yan siyasa duk ‘dodo ɗaya su ke wa tsafi’, wato dukkan su abokan juna ne masu tseren rige-rigen kaiwa ga dukiyar al’umma kawai.

A kan haka sai ya ja hankalin jama’a cewa su guji nuna wa ‘yan siyasa makauniyar soyayya, domin duk yadda ‘yan siyasa ke gaba ko adawa, wata rana tare za ka gan su, wuri ɗaya kuma a jam’iyya ɗaya.