Assalamu Alaikum, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.
Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa ɗaura aure yana nufin ƙulla wata alaƙa ce da Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya yi umarni da ita. Gaskiya ne cewa (aure) ya kasance daga cikin ɗabi’u na ɗan Adam, to amma duk da hakan Allah Maɗaukakin Sarki ya tsarkake wannan alaƙa wacce daga ƙarshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a ɗauki wannan alaƙa a matsayin wani abu mara muhimmanci ba.
ɗaya daga cikin munanan ayyukan da wasu suka yi shi ne riƙon sakainar kashin da suke yi wa wannan alaƙa da rashin ba ta muhimmancin da ya kamace ta. Su dai turawa suna mu’amala ne da wannan muhimmin lamari, wannan wata alaƙa ce mai ƙarfi tsakanin mace da namiji, mu’amala tamkar ta cire riga ko kuma shiga wani shago, wato a matsayin wani abu kawai mai sauƙi kana iya yinsa yanzu ka kuma canja shi duk lokacin da ka ga dama. Don haka wannan aƙida ta kan sanya shu’uri da ɗanɗanon mutum su kasance masu adawa da ci gaban wannan alaƙa ta auratayya. A duk lokacin da ɗaya ɓangaren (macen ko namijin) ya ga wani abu ko kuma suka fuskanci wata matsala, to ba tare da haƙuri da la’akari da wasu abubuwa ba akan kawo ƙarshen wannan alaƙa (mai tsarki). Amma shi kuwa addinin Musulunci bai yarda da hakan ba, (wato baya kwaɗaitar da hakan) don kuwa a Musulunci an gina tushen iyali ne bisa ƙarfafan tubalai. A koda yaushe Musulunci ya kan ja kunnen mabiyansa wajen yin taka-tsantsan a lokacin da suke ƙoƙarin zaɓen abokin zama ko kuwa abokiyar zama sannan da kuma yin duk abin da mutum zai iya wajen kiyaye wanzuwar wannan tsarkakakkiyar alaƙa. Dole ne ku yi iyakacin ƙoƙarinku wajen kare wannan sabuwar alaƙa, kamar yadda kuke kula da sabbin tsirran da kuka shuka don su girma su zama bishiyar da za ku amfana da ‘ya’yanta.
Yana da kyau a fahimci cewa, kula da wannan alaƙa ba ta na nufin irin kuɗin shigan da mutum yake samu, ko kuma yawan ilminsa ko kuma irin aikin da yake yi kawai ba, don kuwa shu’urin ɗan Adam kan aure da gina iyali kusan abu guda ne, babu wani gagarumin bambanci tsakanin masani, malami, ɗan wasa, ko kuma lebura da dai sauransu, hakan kuwa saboda shu’urin guda ne tsakankanin dukkan mutane, babu wani bambanci tsakanin talaƙa da mai kuɗi.
Babu shakka kowani guda daga cikin miji da mata suna son gidansu ya kasance wajen kwanciyar hankali da nitsuwa gare su bayan sun gama aikace-aikacensu na rana, wannan wata buƙatuwa ce da ma’auratan suke buƙatuwa da ita a rayuwarsu ta aure; suna buƙatuwa da farin ciki da yanayin da yake samar da hakan. Mai yiyuwa ne (macen ko namijin) su kasance ‘yan kasuwa, ko kuma ‘yan siyasa ko kuma suna zama ne a gida don tarbiyyantar da yara, kai ko ma dai wani irin aiki suke yi, dukkansu sukan gaji, to a lokacin da suka dawo gida, suna buƙatar yanayin cikin gida mai faranta rai, wannan kuwa ba wata buƙata ce ta wuce guri ba, a’a, a ɗabi’ance haka lamarin yake.
Haƙiƙa lamarin ba shi da alaƙa da abin hannun da mutum ya ke da shi, don kuwa akwai da dama daga cikin masu abin hannun da ba su ɗanɗani daɗin zamantakewar aure ba, rayuwarsu ta kasance cikin ƙunci, cike take da hassada da haramtattun buƙatu da fata. Babu shakka mutumin da ke da wani mukami, wanda yake ba da umarni, ya kan iya fuskantar matsaloli daban-daban a gida, me yiyuwa ne shi wannan mutum ko kuma wannan matan ya/ta samu abokin zama mai saurin fushi, mara haƙuri ko kuma malalaci. Don haka dukiya, mukami, zaman birni ko ƙauye ba za su canja yanayin zamantakewar iyalai ba matuƙar dai babu fahimtar juna da yafewa tsakanin ma’auratan biyu. Don haka ne ma Allah Maɗaukakin Sarki cikin Alkur’ani mai girma yake cewa: “Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai guda, Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami nitsuwa da ita…” (Suratul A’araf 7:189). Abin da Alkur’ani yake nufi shi ne ‘mu’amala da juna cikin ƙauna da kuma samun kwanciyar hankali da juna’. Lalle ya kamata mata da miji su kasance hanyar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ƙauna tsakanin junansu, don haka dole ne ya ku matasa maza da mata ku sanya hakan cikin zukatanku, don kuwa aurenku zai kasance sanadiyyar haifar da iyali. Dole ne gidan da za ku zauna ya kasance waje ne na kwanciyar hankali da nitsuwa gare ku da kuma ‘ya’yan da za ku haifa.
A tare mu a mako na gaba… Wassalam
Daga Mustapha Musa Muhammad a Kaduna, 08168716583
