Rayuwar gidan haya

Spread the love

Ina magana ne daga Jiharmu, Jihar Katsina domin a shekaru 30 zuwa sama duk wanda zai yi aure ba zai bazama neman gida ko ɗakin haya kamar a yau ba. Na samu kaina a zaman haya daga shekara ta 2000 zuwa 2002 wanda kafin in mallaki nawa gidan na fuskanci yadda rayuwar haya ta ke. Dillalai a kula; haka nan ku waɗanda ke gina gidaje ku ba da haya duka a riƙa sanya tausayi da sauƙaƙawa. Mutum ne zai zo neman gida ko ɗaki na haya za a gindaya masa wasu sharuɗɗa duka ya cika kuma kuɗi ya bada amma idan an damƙa masa makullai zai taras gidan na da buƙatar gyare-gyare wanda a tsakanin mai gidan da dillalin gidan duka sun san da hakan. Duka sai mun riƙa fahimtar idan mun tausaya ma junan mu rayuwa za ta inganta kuma aminci ya yawaita a tsakanin mu. A Katsina akwai wani mutum wanda yana da gidaje na haya amma idan ka amsa kafin ka shiga zai yi gyare-gyare da fanti duka da aljihunsa. Allah ka ba mu ikon gyarawa ta kyautatawa. Ameen.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519\08080140820.

By ukarofi