Sheikh Giro yana nan raye, inji makusancinsa

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Shugaban makarantar Uthman bin Affan da ke garin Argungu a Jihar Kebbi, Malam Nasiru Abubakar Mera, ya ƙaryata labarin mutuwar Shehin Malamin Addinin Musulunci Sheikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu da labarin mutuwarsa ya mamaye kafafen yaɗa labarai na sada zumunci a safiyar jiya Alhamis.

Malam Nasiru Abubakar Mera, wanda makusancin shehin malamin ne wanda a lokacin da ya ke zantawa da Wakilin Blueprint Manhaja ta wayar tarho ya nuna rashin jin daɗinsa bisa ga irin yadda musulmi ke ƙirƙiro ƙarya saboda kawai ya tayar da hankalin Musulmi.

Ya ƙara da cewa Malam Giro yana nan cikin ƙoshin lafiya hasali ma jiya Alhamis ya fita wajen waɗansu hidimomi na addini kamar yadda ya saba.

“Wannan aikin kaɗa’an haramun ne a Musulunci, saboda haka Ina kira ga masu irin wannan ɗabi’ar da su ji tsoron Allah,” inji shi.

Haka zalika Lauwali Adamu Yeldu tsohon shugaban ƙungiyar Izala a ƙaramar hukumar mulki ta Argungu kuma ɗaya daga cikin dattijawan ƙungiyar ya ƙaryata wannan labarin na mutuwar shehin malamin inda ya bayyana cewa Malam Giro yana nan a raye kuma lafiya ƙalau.