Gidauniyar Action Aids ta gudanar da taron ranar matasa ta duniya

Daga BABANGIDA S GORA a Kano

Alhamis da ta gabata gidauniyar da ta ke gudanar da aikinta ƙarƙashin uwar ƙungiyar ta ƙasa watau Action Aid ta bi sauran ƙungiyoyin duniya wajen gudanar da taro kan hanyoyin da matasa za su bi don samun hanyoyin da za su zama mafita a rayuwarka ta yau da kullum.

Da ta ke jawabi yayin taron daraktar gidauniyar ta ƙasa, Ene Obi, ta yi matuƙar farin ciki da irin yadda al’umma jihar kano suke ba wannan ƙungiya goyon baya tare da da haɗin kai da ya samo asali wajen jajircewar shugaban wannan gidauniya da sauran ma’aikatan ta na jihar wajen shiga lungu da saƙo na Kano don yaɗa manufar wannan ƙungiya.

Sannan Mrs Ene Obi ta ce a Nijeriya, Kano na da mutane kashi 59.43 bisa ɗari da ba su da aikin yi a kwata ta biyu a wannan shekara ta 2022 da ya ke babban ƙalubalene ga al’ummarmu da mu kanmu da zai iya kawo matsalar rashin zaman Lafiya.

Sai dai Kuma Ene Obi tasanar cewa, abin alfahari a yanzu shi ne a yunƙurin da wannan gidauniya ta ke da sauran ƙungiyoyin duniya ya sa matasa na ƙara fahimtar suwaye su da kuma hanyoyin da za su taimaki kansu ko dogaro da kai.

Shi ma a nasa jawabin mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayaro da ya samu wakilcin Ɗan Majen Kano yayin gudanar da taron na ranar matasan ta duniya ya fara godiya ga wannan gidauniya ta Action Aids bisa ƙoƙarinsu na samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai da kaucewa abin da ya ke kawomana tashin hankali a halin yanzu.

Sarkin ya kuma shawarci matasan da su zama masu neman nakansu da zai iya magance matsalar da aka fi kallonsu da ita ta shaye-shaye harkar daba da kuma bangar siyasa harma da harkokin garkuwa da mutane dan kuɗin fansa da a yanzu ya zama ruwan dare a Nijeriya.

Kazalika Mai Martaba ya kuma buƙaci, ƙungiyar ta Action Aids takara faɗaɗa ayyukanta zuwa dukkan ƙananan hukumomin Jihar Kano don cigaba da wayarma jama’a kai da fahimtar da su hanyar da za su bi don kauce wa hargitsi da cece-kuce, yayin da kuma ya qara buƙatar cigaba da shiga jaridu da Radiyo Talabijin don ƙara wayar wa da al’umma kai.

Shi ma a nasa jawabin tunfarko shugaban tafiyar na Jihar Kano Alhaji Dr.Muhammad Mustapha ya yi matuƙar godiya ga Allah da ya ba su damar gudanar da wannan taro a kuma wannan rana ta matasa da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fidda don zama da jin irin cigaba da matsalolin da matasa suke samu tare da samo hanyoyin magance su.

Sannan Dakta Muhammad Mustapha ya ce, ƙoƙarinsu shi ne koda yaushe mata da matasa su zama kan gaba wajen tafiyar da harkokin rayuwa tare da sannin illolin da sukan iya faɗawa yayin gudanar da wasu ayyukan da na sani da zai iya sa su cikin ƙunci na rayuwa.

Cikin waɗanda suka samu halartar taron akwai Wakilan gwamnati, jami’an tsaro da masu riqe da sarautun gargajiya da masu ruwa da tsaki da dai sauran al’umma daban.

Taron dai yagudana a ɗakin taro na ‘The Avenue Event Center’ dake kusa da asibitin Nasarawar a Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *