Ruwan sama ya zauna, taki ya tashi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A can tarihin noma ba batun takin zamani. Wannan ma kai tsaye shi ya sa a ka ambace shi da takin zamani. Abun da mu ka sani shi ne a zamanin can baya a na amfani da takin kashin dabobi ne da ma kwasar bola a kai gona don ƙarfafa kyan yabanya.

Wancan takin a kan kira shi da na gargajiya kamar yadda a ke zayyana magungunan kauci da sayu a matsayin maganin gargajiya. Kazalika a shekarun baya akwai wadatar filayen noma masu lafiya da ba sa buƙatar taki mai yawa wajen samar da yabanya.

Ba ma haka kaɗai ba manoman da ma mutanen da ke buƙatar abincin ba su da yawa. Lokacin da mutane ke da wadatar filayen noma su kan yi amfani da canja fili a shekaru 6 don barin wani sashe ya huta. Duk filin da za a riƙa bari ya huta shekaru 6 kafin noma shi ba shakka zai samar da yabanya mai kyau.

Yanzu a na fafutukar samun filayen gona da na gina gidaje da kamfanoni ne ko ma masu samun gandun daji gaba ɗaya su kewaye da waya su ce gidan gonarsu ne ko da kuwa ba sa noma wani abun kirki a ciki sai dai kawai jin cewa sun a mallakar manyan gonaki.

Gaskiya da dai a na samun noma manyan gonaki yadda a ke mallakarsu, da ba shakka za a samu wadatar abinci. Gaba ɗaya a noman talaka da bai fi hantsi biyu yakan iya samun masara ko geron kunu na wani lokacin shekara ne inda zai sayar da ɗan waken da ya samu don samun na cefane ko sayen taki don noman wata shekara in rai ya kai.

Duk labarun da mu ke samu na nuna taki ya gagari gonar talaka. Hatta kashin dabbobin ma babu tun da an samu jarrabawa a kiwon shanu. Bolar kuma da za a iya kwasa a kai daji ba motar ɗiba. A birane ma yanzu ba a samun irin bola ta zamanin da da a ke kira juji inda a kan tona a samu gwazarma.

In ka zaga za ka gadan filin da ka sani juji ne a da can ya zama wani gidan sama ko titin mota. Rashin wajen zuba bolar nan a yawancin wajaje ya sa gwamnati ware wasu ’yan sassa na zuba sharar kafin mota ta zo ta kwashe. An ma kafa wasu kamfanoni da ke da masakan zuba shara da su kan zo su kwashe in wata ya yi a biya su. Kwasar bola babbar sana’a ce a zamanin yau.

Tun tarihin kafuwar Nijeriya ba a tava samun shekarar da takin zamani ya yi tashin gauron zabi ba kamar bana. Na ji gwamnatocin wasu jihohi ma na murnar sanar da jama’a sun samar da takin zamani a farashi mai rangwame kimanin Naira dubu 19!, in mutum ya shiga kasuwa don sayen taki kuma ya samu kan Naira dubu 25. In da za a ce ma a na samun wadataccen takin zamanin na gwamnati da da dama-dama.

Gaskiya gwamnati na bayyana shirye-shiryen raya noma ta hanyar ba da tallafin noma da ma samar da kayan aikin noman. Kamar yadda a ke ta maganar rashin samun matatun man fetur masu inganci a Nijeriya da ya sa sai lalle an shigo da man daga ƙetare, haka ya dace a bincika shin Nijeriya ba za ta iya kafa manyan kamfanonin samar da takin zamani ba ne? shin kayan da a ke haɗa taki da su na da tsada ko ma sai an shigo da su daga ƙetare ne?

Binciken da na gudanar a wasu jihohi na bayyana cewa su na cewa su na da kamfanonin takin zamani amma gaskiyar lamarin kamfanonin cakuɗa taki ne ko zuba shi a buhu bayan an shigo da shi daga ƙetare. Ƙasar Maroko na daga ƙasashen da a kan shigo da takin zamani zuwa Nijeriya.

Har dai akwai tsari mai kyau ya dace a bunƙasa fasahar samar da taki zamani mafi inganci da ya dace da irin filayen noman Nijeriya. Jami’o’in Nijeriya da cibiyoyin nazarin lamuran noma za su iya wannan aiki.

A gwada sanya kwararru kan wannan fage a gani ko za a samu gagarumar nasara ta samar da taki mai araha kuma wadatacce ga ƙanana da manyan manoma. Don duk mun amince cewa a yanzu noma ba zai yi nasarar da a ke buƙata ba in ba tare da taki ba.

An ƙirƙiro hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasa amma kai tsaye abun da kan amfani talaka tsawon shekaru tun ma ba a kafa ƙasashen mu ba, noma da kiwo ne. Tun da noma na gudana cikin tangarɗa don ba taki kiwo kuma ya shiga yanayin gallafiri don yadda fitinar rashin tsaro ta kutso cikin jama’a.

Ƙalubale ne babba a ke fuskanta da kan kawo tsananin ƙuncin talauci. Illar talaucin zamanin yau na tafiya ne ta yadda abinci ya gagari talaka, abincin kuwa ko ga garin rogo ne. A shekarun baya a kan yi fama da talauci amma talakawa kan ci su ƙoshi ko da abincin ba nama.

Don haka ya zama mai muhimmanci a ɗauki kwararan matakan da za su yi tasiri kai tsaye kan bunƙasa noma da kiwo. Mutanen yankunan karkara da dama kan dogara kan noma ne wajen samun abinci da abun biyan buƙata.

Idan gwamnati ta inganta noma da kiwo za ta samu saukin kula da al’ummar ta don hatta wasu matsalolin rashin tsaro na shiga sharo ba shanu za su ragu. Babbar hanyar yaƙi da talauci na haɗe da inganta noma.

Hukumomin bunƙasa aikin noma na tarayya da na jihohi, ya dace su riƙa aiki tare har ma ya kai ga malaman gona da kan shiga har cikin gonaki don gano mafi sauƙi da ingancin hanyoyi da za a dawo da noma kan yanayin da a ka gada a tarihi.

A kan yi wa noma kirari da ‘na duqe tsohon ciniki kowa ya zo ma duniya kai ya tarar’, da hakan ke nuna sana’a ce mai dogon tarihi a rayuwar mutane. Don haka duk sana’ar da tun a tarihi mai tsawo ta na nan kuma har yanzu a na yin ta ya na rayuwa za ta cigaba da wanzuwa da ita har ƙarshen zaman duniya.

A kan samu sauye-sauye ne ta hanyar ɓullo da dabaru da za su riƙa sanya noman ya zama mai sauƙin yi. Dabarun nan kuwa saboda tsadar su kamar amfani da tarakta, injin shuka ko girbi na hana ƙananan manoma amfana daga gare su.

Har gobe akasarin manoman mu masu fafutukar ciyar da kan su kan yi amfani da fartanya ne ta hannu da garmar shanu da sauran su wajen noman su. Idan har za a taimaki manoma ko da ba za a samu manyan na’urorin noma ba, to a samar da ingantaccen iri da taki mai matuƙar rahusa.

Haqiqa inda labarun jam’iyyun gama-kai na manoma da kan samu tallafin noma ta hanyar lamuni. In an tsananta bincike za a fahimci akasarin manoma ba sa kan wannan tsari don sun fi fahimtarsu shiga kasuwa su sayo taki, iri da sauran kayan noma su nufi gona don aikinsu. Kuma na sha samun labarun wasu da kan karɓi lamunin noma na amfani da shi wajen wasu ayyuka daban ba noma ba.

Duk hukumomi ko ƙungiyoyin da ke ba da lamunin ya dace su tabbatar da duk wanda zai amfana daga lamunin ya zama manomin ne hakanan a riqa bin manoman ko waɗanda a ka ba wa lamunin don ganin wa imma noma su ka yi da kuɗin ko kuwa a’a.

Wani abun ma shi ne wasu kan yi amfani da lamunin wajen gyara gidajen su ko ma zubawa a harkokin kasuwancinsu da tunanin sun ci bulus ba wanda zai tambaye su. Ina ganin ya dace a zayyana iya lokacin lamuni da lokacin dawo da shi.

Idan waɗanda su ka dau lamuni su ka dawo da shi, za a sake ba wa wani rukunin waɗanda ba su amfana ba. Bin diddigin wannan tsarin na lamunin na da muhimmanci ainun. Ta yaya za a ba wa mutum lamunin noma amma sai ya sayi mashin ko mota?, wannan bai dace ba ko kaɗan tsakani da Allah.

Gyaran ya dace ya taso daga sama har can ƙasa ya zama kowa da ke cikin lamarin ya aminta daga faɗawa duk wani yanayi na ha’inci. Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su shiga wannan ɓangare su bincika don gano yadda lamarin ya ke tafiya da yin gyara a inda a ka samu tangarɗa.

Kammalawa – ruwan sama a Abuja:

Ruwan sama ba yankewa na sauka a Abuja ko ina ya jike jagaf da ruwan da zai yiwa shuka amfani ainun.

Tun shigowa watan nan na Agusta, ba a samu irin wannan ruwan ba da ya shafi kowane sashe na birnin inda mutane su ka ɗauko lema don samun shiga shaguna da sauran sassa na hada-hadar yau da kullum.

Da hasken safiya a ka riƙa ganin duru-duru irin na asubahi da ya sa mutane kunna wutar mota don gujewa afkuwar hatsari.

Haƙiƙa direbobi marar sa na’urar sanyaya mota da za ta iya goge numfashi daga jikin gilashin sun sha fama don ƙoƙarin tuki a yanayin mai wuyar tafiya daidai ba tare da faɗawa fargaba ba.

Masu sayar da robobin goge gilashi na baje hajarsu don ganin kasuwa ta buɗe a sakamakon wannan ruwa mai yawa.

Na samu labarin irin wannan ruwan ya isa sassa daban-daban na Nijeriya da ya nuna ruwa ya zauna amma taki ya tashi.