Ba mu jan ragamar mulki haka sakaka, inji Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya bayyana cewar, gwamnatinsa ba za ta ja ragamar mulki da sulhuntawa da son zuciya ko bin tafarkin rashin gaskiya ba, sai ta hanyar bin tsarin shari’a, zayyanannun al’adu da kuma wasu yanayi.

Kamar yadda gwamnan ya ce, ana tabbatar da kyakkyawan mulki ne ta hanyar bin dokoki, don haka ya kasance wajibi a gudanar da mulki ta tsarin bin doka, samar da ƙwararrun ma’aikata, haɗi da kuɗaɗe domin tafiyar da gwamnati cikin sauƙi.

Gwamna Bala yana yin wannan jawabi ne a yayin da yake rattaɓa hannu akan wasu ƙudurorin dokoki guda 12 da majalisar dokoki ta jiha ta zartar, yana mai danganta wannan nasara ga haɗin kan cimma burace-burace a tsakanin ɓangarorin majalisar dokoki da majalisar zartarwa na gwamnati, kamar yadda suka dauwamar da jera tafiyar cimma manufofi bai ɗaya domin amfanin jama’arsu.

“A matsayin abokan jera tafiya cikin fafutukar cigaba, ɓangarorin guda biyu suna da manufofi waɗanda suka yi kama da juna na gudanar da gwamnati bisa tafarkin bin dokoki kamar yadda zamani ya kawo a tafiyar duniya bai ɗaya da zummar bin ƙa’dojin doka.

“Wajibi ne mu aro daga zayyanannun ƙa’idoji na wasu tafarkai kamar yadda muke yi a halin yanzu a cikin wa’adojin majalisar dokoki da majalisar zartarwa, za mu jinjina wa kan mu a kowane lokaci bisa hangen nesan mu, da yin amfani da ilimi bisa mujadalar ilimi da kyawawan tsare-tsare, don haka ne a yau muke rattaɓa hannu akan waɗannan ƙudurorin doka domin su kasance dokoki na yin aiki da su.”

Ya kara da cewar, “Ina farin cikin ni da abokina muƙaddashin gwamna, Sanata Baba Tela, muna amfani da ƙwarewar mu, muna aiki kafaɗa da kafaɗa da majalisar dokoki, domin gudanar da ayyuka kan ta farkin doka”.

Mohammed ya kuma sanya hannu a ƙudurin dokar da ta soke dokar kafa Jami’ar Jihar Bauchi da kuma wanzar da dokar kafa Jami’ar Sa’adu Zungur, wacce ta kasance batun canjin suna ne kaɗai bisa shawarar majalisar zartarwa ta jiha, yana mai bayyana cewar, Marigayi Malam Sa’adu Zungur mutum ne kamili mai matuƙar mutunci, ɗan kishin ƙasa, kuma masani da ya yi fice.

Marigayi Malam Sa’adu Zungur da Sakatare-Janar ne na jam’iyyar “National Council of Nigeria and Cameroon” (NCNC), jam’iyyar siyasa da shi, Dokta Nnamdi Azikwe, Shugaban Jumhuriyar Tarayyar Nijeriya na farko bayan da ƙasar ta samu ’yanci daga turawan mulkin mallaka.

Gwamnan ya yaba wa majalisar dokoki ta jiha bisa ƙoƙarinta da ɗaukar nauyin amincewa da waɗannan dokoki da aka aike mata, yana mai bayyana zumunta dake a tsakanin majalisar dokoki ta jiha da majalisar zartarwa abin a yaba ne, tare da fatar zumuntar za ta ɗore domin amfanin jama’ar jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *