*Janar Dambazau ya nemi a tsaurara matakan yaƙi da ta’addanci
Daga AMINA YUSUF ALI
Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Laftana Janar Abdulrahman Bello Dambazau (mai ritaya), ya yi kira da a yi garambawul a sashen tsaron ƙasar nan domin magance ƙalubalen tsaro da suke fuskantar ƙasar nan.
Dambazau ya qara da cewa, dole ne a yi nazari na gaggawa a kan salon yaƙi da ta’addancin da muke da shi a Nijeriya, musamman ma saboda yawaitar samun ɓata-gari masu shigowa daga wajen Nijeriya, abinda a cewar sa ya jefa rayuwar ‘yan Nijeriya a cikin tasku.
Tsohon ministan ya yi wannan jawabi ne a ranar Talatar da ta gabata a yayin gudanar da taron lacca da ba da lambar yabo na shekara-shekara da kamfanin Blueprint ya saba gudanarwa. Inda aka gabatar da lacca mai taken: ‘Siyasar 2023: Tsaron ƙasa da cigaban Nijeriya.
Garambawul ɗin da yake nufi a cewar sa ba wai kawai a magance rashin haɗin kai da rashin tsaro a tsakanin hukumomin tsaro ba wanda a ganin shi ne babban naƙasun da ya hana daƙile ayyukan ‘yan bindiga na waje, amma zai matuƙar taimakawa ba kaɗan ba wajen ƙara wa hukumar ƙwarin gwiwa.

Ya koka da yadda ƙasa da jami’an tsaro guda 200,00 (jami’an sojin ƙasa, sojojin ruwa da na sama) za su iya tsaron lafiyar ‘yan Nijeriya fiye da mutum miliyan 200. Sun yi matuƙar kaɗan a cewar sa.
Tsohon ministan ya ƙara da cewa, sama da jamian ‘Yansandan Nijeriya guda 400,000 ba a amfani da su a inda ya kamata. A cewar sa yawancin ayyukan tsaro sojoji ne suke gudanar da shi su kaɗai.
Sannan a cewar sa, bayan gyaran kuma, akwai buƙatar ihsani ga jami’an tsaron don kula da walwalarsu da kuma samar da amana tsakaninsu da al’umma shi ma yan daga abubuwa masu muhimmanci da za a yi amfani da su don tunkarar matsalar rashin tsaro kuma su dawo da martabar hukumomin tsaron da ta zube a idon al’umma.
A cewar sa, a wani lokaci can baya wasu shugabannin sun ƙoƙarta. Kamar Obasanjo ya tava shigo da wani tsari na bincike a kan jami’an sojoji.
Dambazau ya qara da cewa, shi ma Janar Martin Luther Agwai, ya zo da wani tsari na canza tunanin mutane gane da jami’an tsaro ganin yadda daɗewar sojoji a mulkin ƙasar nan ya jawo varna mai yawa.
Don haka a cewar sa, gyara sashen tsaro ya zama wajibi domin tunkarar matsalar tsaron da ake ciki da wacce za a shiga nan gaba. Kuma abu ne da yake buƙatar a fara yi ciki hanzari.
Kuma abu ne da ya kamata ya zama na farko a jerin abubuwan da gwamnati mai zuwa za ta fara aiwatarwa idan ta shiga ofis a watan Mayun shekarar 2023. Don babu wani zaɓi sai an aikata hakan.
“Bayan abubuwan da na lissafi tun da fari, wasu manyan dalilan da suka sa dole a yi gyara a sashen tsaron sun haɗa da:
Na farko, alamomi sun nuna sam ba haɗin kai da fahimtar juna tsakanin hukumomin tsaron a yayin da suke gudanar da ayyukansu kowa yana cin gashin kansa ba tare da taimakekeniya ba. Sannan suna ɓoye wa junansu bayanan sirri kai ka ce gasa suke a tsakaninsu”. Inji shi.
“Abu na biyu, akwai ƙarancin bin diddigin al’amuran tsaro. Abinda ya sa riƙon gaskiya da amana yake matuƙar wahala a sashen” a cewar sa.
Sannan wani babban dalilin shi ne, yadda sojoji suke gudanar da al’amuran tsaro kusan dukkansa.

Hukumar ‘Yansanda ta zama kawai ‘yar amshi shata; ɗaya daga cikin ƙafafunsa masu rauni wato ita da kotu da kurkuku. Wanda ba wani ƙarfi aka ba su sosai ba shi ya sa ake ta samun yawaitar aikata laifuffuka a Nijeriya.
Bugu da ƙari, akwai buƙatar a ƙara ƙarfafa ƙarfin hukumomin tsaron ta yadda za su iya mayar da martani a take idan buƙatar hakan ta taso. Tare da wadatar kayan aikinsu kuma a kowanne mataki.
Hakazalika a cewar sa, shi ma samun yardar al’umma yana da matuƙar muhimmanci wajen gyara al’amuran tsaron. Domin jami’an tsaro ba su da isasshen ƙarfin tunkarar wannan kuma ƙari ne a kan aikin da yake gabansu na kare martabar ƙasar Nijeriya mai girman kilomita 923,768 da yawan al’ummar da suka zarta miliyan 200.
A wannan yanayi, hukumar Soji ta samu kanta a halin aiki ya yi mata yawa kuma ga rashin wadatar kuɗin da za a gudanar da ayyukan dukka.
Su kuma hukumar ‘yansanda sam ba amfani da su yadda ya kamata, abinda ya ƙara kawo rashin bin doka a ƙasar nan.
Daga cikin ‘Yansanda 400,000 da suke ƙasar nan an rarraba su zuwa masu kariya ga ɗaiɗaikun mutane, ko kamfanoni/ma’aikatu da ƙungiyoyi masu zaman kansu maimakon amfani da su ta hanayar tsaron ƙasa don a samu haɗin kai su yi aiki tare da sojoji.
Game da zaɓen 2023:
Dambazau ya bayyana cewa, bayan zavuvvuka 6 da aka yi a Nijeriya, zaɓen 2023 zai kasance karo na 7. Kuma a cewar sa, daga cikin abubuwan da za su yi tasiri a zaɓe mai zuwa akwai, ɓangaranci, addini da sauran abubuwa da za su yi tasiri a kansa.
Ya shawarci ‘yan Nijeriya da su kasanceasu mayar da hankali a kan abubuwa masu muhimmanci a yayin zaɓen kamar; Rage talauci, samar da ingantacciyar lafiya, da sauran abubuwa. Bai kamata a ɓata lokaci a kan banbancin addinin a ƙabilanci ba.
Game da harin gidan kurkuku Kuje a Abuja:
A game da harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da na gidan gyara hali na Kuje, Dambazau ya bayyana cewa, waɗannan hare-haren sun nuna cewa, ‘yan ta’addar suna da mafaka kusa da birnin Tarayyar. Ma’ana, a jihohin Kogi, Kaduna da kuma Neja, inji shi.
Haka zalika, ya yi kira ga jami’an tsaro da su cire tsoro su iske su a maɓoyarsu su hana musu samun kwanciyar hankali. Domin daga irin hare-haren su na kwanan nan ya nuna maɓoyarsu ba za ta wuce kusa da Abuja ba. Wato a jihohin Kogi, Neja, ko Kaduna.
Sannan game da masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda, ya kamata a samar musu mummunan hukunci wanda zai zama izina ga yan baya. Bai kamata mu ƙyale azzalumai su mamaye mana gari ba, tare da jefa tsoro a zukatan mutane.
Kuma dukkan al’umma su ba wa gwamnati gudunmowa wajen yaƙi da ta’addanci yayin da za a cigaba da mai da hankali ga kakar zaɓen ta shekarar 2023″.
Amma a cewar sa, ƙyale su su ci karensu ba babbaka yana daga abubuwan da suke ƙara musu ƙwarin gwiwa. Don haka a takura musu a hana su sakat. Kuma a kawar da su a duk lokacin da dama ta samu.
“Dole a bar mu mu yi rayuwarmu yadda muke so ba tare da wani ɓata-gari can ya hana mu walwala ba”. Inji shi.

Shi ma a nasa jawabin, mawallafin Blueprint, Kakaaki Nupe, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga gwamnatin Tarayya a kan ta ƙara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a ƙasar nan.
Kakaakin Nupe ya yaba wa dukkan hukumomin tsaron ƙasar a kan jarumtarsu wajen tunkarar walubalen dake fuskantar ƙasar. Sannan ya yi kira da gwamnati ta haɗa kai da al’umma don magance matsalar rashin tsaro a ƙasar. Domin ceto al’umma daga sharrin yan ta’adda da yan bindiga da sauran ɓata-gari.
Haka zalika, ya ƙara da cewa, bai kamata a bar matsalar tsaro ta shafi harkar zaben da za yi a shekarar 2023 ba.