NBC ta ɗaga wa kafofin da ake bi bashi ƙafa zuwa 23 ga Agusta

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta dakatar da shirinta na garƙame tashoshin rediyo da talabijin faɗin a ƙasa zuwa wani ɗan lokaci.

Hakan ya faru ne sakamakon saka baki da Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da Ƙasa (IPI) reshen Nijeriya ta yi don samar da maslaha.

Tun farko, NBC ta lashi takobin ƙwace lasisin wasu gidajen talabijin da rediyo a faɗin ƙasa kimanin su 52 bashin da ake bin su bashi sakamakon ƙin sabunta lasisinsu.

Yanzu dai NBC ta ce ta bai wa kafofin da lamarin ya shafa zuwa ƙarfe shida na yamma na ranar Talata, 23 ga Augusta kan su biya bashin da ake bin su ko kuma ta ɗauki matakin da ya dace a kansu.

Tun bayan da NCB ta ba da sanarwar shirinta cibiyar IPI ta nemi zama da hukumomin da suka dace don shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi.