Shekaru 40 bayan Ƙalarawi ya ce malaman Kano da ’yan kuntuku ɗaya suke wajensa

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ

Allah ya ji ƙan Malam Lawan Ƙalarawi, matasa da dama ba su san shi ba, amma ba na jin an taɓa yin malami a zamaninmu kamarsa. Dalili kuwa shine ba ka taɓa ganin malami da ke faɗar gaskiya ba jin tsoro ko saboda wata alaƙa ta kusanci da za ta hana shi faɗar gaskiya ba.

Bayan nan kuma, mutum ne mai tsananin hikima da falsafanci yadda ya ke iya hasaso me zai faru a gaba. Sakamakon wannan ɗabi’a tasa, kuma ya yi shura a zamanin mulkin sojoji, babu wani mai mulkin soja da bai caccaka a kan mumbarinsa ba, ballantana malamai waɗanda ya ke gani sun yi ba daidai ba. Daga inda ya ke wa’azi a filin Shahuci, idan ka ruga da gudu, ba za ka tsaya ba sai ka je Gidan Kabara (Gidan Ƙadiriyya), wato muhallin Sheikh Nasiru Kabara, amma idan ya dinga caccakar Malam Nasiru sai ka ji ba daɗi.

A wannan lokaci babu wani malami a Kano da ke da almajirai irin na Malam Nasiru Kabara, kuma idan da zai umarci almajiransa sai sun yi fata-fata da Malam Ƙalarawi, amma saboda tarbiyya irin ta da, ko martani ya hana su yi wa Ƙalarawi.

Malaman Kano sun yi yunƙuri da haɗin kan gwamnatin mulkin soja domin hana Ƙalarawi yin tafsiri ta hanyar haɗa kwamiti, inda wasu manyan malamai tara daga ɓangarori daban-daban domin su tantance masu wa’azi, inda aka gayyaci Ƙalarawi.

Wannan ƙoƙarin ne ya sa Ƙalarawi ya yi wa waɗannan malamai laƙabi da cewa ba su da bambanci da ’yan kuntuku (su ne yaran masu kalangu da ke buga ’yar ƙaramar ganga da sauri). Wato ya na nufin sun zama ’yan amshin shata kawai na gwamnati, yadda ake amfani da su don a daƙile wani abu.

Shi ya sa Malam Ƙalarawi ya yi fice cikin malaman Kano a wancan zamani yadda ya ke iya sukar sojoji masu mulki, manyan malamai irinsu Nasiru Kabara, attajirai irinsu Ɗantata da sarakuna irinsu Ado Bayero, domin ba ya zuwa gidan kowa neman alfarma ko kwaɗayi. Wannan ya sa ya ke iya faɗa da dukkan ‘elites’ a kan gaskiya ya zauna lafiya.

Malami ne mai kamar ɗan gwagwarmaya, kuma haka kowane malami mai tsoron Allah ya kamata ya kasance. Malamai su ya kamata su zama garkuwar talaka a hannun mahukunta, amma saɓanin haka ke faruwa yanzu. Malamai ba sa kare muradin kowa sai na mahukunta, saboda sun zama tamkar “Yan Kuntuku”.

Wannan gwamnatin ta Tinubu babu wanda ya samar mata da ƙuri’a a Arewa sama da malamai, yadda su ka ɓuya bayan Muslim-Muslim. Amma ba sa iya faɗa wa gwamnati gaskiya, saboda ta siye su ta biya, kuma su ke ƙoƙarin hana talaka ya nemi haƙƙinsa.

Na yi imani akasarin waɗanda ke ƙyamar a yi wa wannan gwamnatin zanga-zanga, ko dai sun jahilci haƙƙin masu mulkin kan talakawansu, ko kuma su na cikin masu morar tsarin da gwamnati ke bi, ko kuma waɗanda ba su cikin matsala ne, don haka babu ruwansu da matsalar wani. Amma wallahi duk wanda ya yi imani da Allah, ba zai so ya ga ’yan Nijeriya a cikin ƙuncin da wannan gwamnati ta jefa talaka ba gaira ba dalili.

Babban abin takaici da mutane ba su fahimta ba shine, ta yaya gwamnati za ta sami ƙarin kuɗaɗen shiga na kaso 53% a shekarar farko, inda ta rarraba ga tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sama da tiriliyan huɗu (adadi mafi girma a tarihin ƙasar), amma ta talauta fiye da kashi 60 na ’yan ƙasa, saboda janye tallafin mai wanda shi kaɗai da ma talaka ke mora a arzikin ƙasar. Kuma su a ɓangarensu babu abinda su ka rage na facaka da dukiyar al’umma. Amma babu wani Malami ƙwaya ɗaya da ya fito ya ce ba daidai ba ne. Sannan an rasa ina rarar biliyan 500 da gwamnatin ta ce duk wata za ta samu ta riƙa ayyuka da shi? Ina ayyukan? Wane malami ne ya bi ba’asi?

Talakawa ana ta tura su bango, yadda a yau Nijeriya ta ciri tutar mafi yawan matalauta a duniya, kuma fiye da kaso 70% a Arewa, amma yayin da su ke yunƙurin fitowa su nuna rashin amincewa da wannan tsari, sai ga malamai sun bazamo suna cewa zanga-zanga haram ce? Malaman da a baya saboda ƙabilanci da bambancin addini su ka goyi bayan yi wa Jonathan zanga-zanga, wadda su Buhari, Tinubu, El-Rufa’i da sauransu su ka jagoranta.

Anya maganar Ƙalarawi ba ta tabbatar da cewa, malamanmu sun zama ’yan kuntuku ba? Zanga-zanga halal ce a addini, saboda Allah ya ce (Q4:148), “Allah ba ya son bayyanawa da munana daga magana, face ga wanda aka zalunta.”

By ukarofi