Shettima ya jagoranci gwamnoni shida zuwa masana’antar tufafin Jamhuriyar Benin don farfaɗo da na jihohin Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yunƙuri na sake farfaɗo da masana’antun samar da kayan tufafi a Nijeriya, gwamnoni guda shida sun ƙudiri aniyar yin koyi da tsarin masana’antu na Glo-Djigbe Industrial Zone (GDIZ) na Jamhuriyar Benin domin ƙarfafa fannin samarwa da bunƙasa masana’antu a jihohinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin sun ci wannan alwashi ne a Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagorance su wajen ziyarar sanya ido a masana’antar da ke Cotonou, wadda ta zama abin koyi wajen amfani da salonta na juya harkokin noma zuwa samar da ababen masana’antu masu yawa.

Wannan ziyara ɓangare ne da ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na samar yanayin da zai bayar da damar samar da hanyoyin amfani da harkokin noma da masana’antun a waje guda a sassan ƙasar, farfaɗo da harkar samarwa da samar da ayyuka daga kayan noma.

Gwamnonin sun haɗa da Gwamnan Imo, Hope Uzodimma; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang; Gwamnan Kwara kuma Shugaban Ƙungiyar gwamnonin Nijeriya, AbdulRahman AbdulRazaq; Gwamnan Katsina, Dikko Raɗɗa; da kuma Umar Namadi na Jigawa.

Gwamnonin sun lura cewa tsarin GDIZ ya nuna yadda tsare-tsaren gwamnati za su yi gudana bisa yadda aka shirya su, samar da ababen more rayuwa masu ɗorewa da inganta lamuran zuba jari na masu zaman kansu ta yadda za a sadar da su da masu aikin noma, rage adadin shigo da ɗanyen kayayyaki da samar da dubunnan ayyuka.

By Babaji

Leave a Reply