Shettima ya maƙala wa ƴan sandan tawagarsa lambobin ƙarin girma

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a ranar Juma’a ya yi bikin ɗora sabbin muƙaman da aka ba wasu jami’an ‘yan sanda biyar daga tawagarsa ta tsaro, bayan samun ƙarin girma daga hukumar kula da aikin ‘yan sanda (PSC). Waɗanda aka ƙarawa girman sun haɗa da Idowu Olatunji, wanda aka daga zuwa Chief Superintendent of Police (CSP), Adamu Barma zuwa Superintendent of Police (SP), da kuma Rufai Mohammed Bello, Usman Abubakar, da Yanas Zidon, da aka ɗaga su zuwa Deputy Superintendent of Police (DSP).

A yayin taron bikin ɗaurin muƙamin da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya yaba da jajircewar jami’an kan ayyukansu, tare da tunatar da su nauyin da ya ƙara hawa kansu sakamakon sabbin muƙaman da suka samu. Ya kuma tabbatar musu da goyon bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen ci gaban jami’an tsaro da inganta jin daɗin su. A cewarsa, “Ƙarin girman da kuka samu alamar an yaba da sadaukarwarku, amma yana nufin ƙarin nauyi kan ayyukanku ga al’ummar Nijeriya.”

Shettima ya yi kira ga jami’an da su ci gaba da kiyaye ƙa’idojin aikin ‘yan sanda, su kasance marasa aibi, kuma su dage wajen bin ƙa’idoji na gaskiya da riƙon amana. Haka zalika, ya gode wa hukumar kula da aikin ‘yan sanda kan gaggawar amincewa da ƙarin girman jami’an.

By ukarofi