Shettima ya tafi Switzerland halartar taron tattalin arziki na duniya

Mataimakin shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, zai halarci taron shekara-shekara na taron tattalin arzikin duniya (WEF) a Davos, inda zai gudanar da tarurruka tare da shugabanni daga ƙasashe daban-daban da kuma shiga cikin kwasa-kwasai da muhawarori da aka tsara don taron.

Daga cikin muhimman abubuwan da za su gudana, akwai wani taron bita mai taken “Tsarin hada-hadar zuba jari don Kasuwannin Afirka,” wanda bankin ci gaban Afirka (AfDB) ya shirya tare da haɗin gwiwar WEF. Wannan taron zai gudana a Cibiyar taro ta Jakobshorn, inda za a tattauna hanyoyin inganta zuba jari a kasuwannin Afirka da nufin gina nahiyar da ta kasance mai arziki, adalci, da kuma dauwamammen ci gaba.

Har ila yau, an tsara wani babban taro don sanar da shirin ‘Humanitarian and Resilience Investing (HRI) Roadmap for Africa,’ wanda bankin AfDB ya ɗauki nauyinsa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shugabannin ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu wajen zuba jari a kasuwannin Afirka. Mataimakin shugaban Ƙasa zai kuma halarci liyafar cin abincin dare tare da shugabannin duniya da sauran manyan baƙi a Kurpark Village, Eiger.

Sanata Shettima zai jagoranci wani taro mai taken “Sauya cinikayyar dijital zuwa tushen ci gaban Afirka,” wanda za a gudanar a Pischa Congress Centre, inda za a tattauna rawar ɓangaren masu zaman kansu wajen inganta yarjejeniyar cinikayyar dijital ta AfCFTA. Bugu da ƙari, zai kasance a wani tattaunawar ƙwararru mai taken “Global Risks 2025” a Aspen 2 Congress Centre, inda za a tattauna ƙalubale na duniya da suka haɗa da siyasa, fasaha, da muhalli. Mataimakin shugaban Ƙasa zai koma Abuja bayan kammala tarukan.