Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji da tarwatsa rumbun makamansa a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun sojoji sun yi nasarar kashe ɗan sanannen jagoran ƴan ta’adda, Bello Turji, a wani hari da suka kai wa maɓoyar ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Zagazola Makama, rahoton da ya fi mayar da hankali akan kawo ƙarshen ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya bayyana cewa jami’an FANSAN YAMMA ne suka gudanar da atisayen.

Rahoton ya ce ne yi rubdugu ne daga jami’an sojin ƙasa da na sama a maɓoyar ƴan bindigar dake Fakai inda Turji da mutanensa suka jima suna addabar al’umma a ƙaramar hukumar Shinkafi dake jihar.

Haka kuma rahoton ya bayyana cewa an kashe ƴaƴan gidan su Turji da wasu manyan kwamandodin dabarsa.

Sannan, an jiyo muryarsa a wata ɗauka ta rediyo inda ya ke neman a kawo masa ɗauki daga wasu jagororin ta’addanci guda bakwai.

Sauran sansanonin da sojojin suka farmaka sun haɗa da Zangon Ɗan Gwandi, Zangon Tsaika, Zangon Kagara da kuma wata makaranta da Turji ya ke amfani da ita wajen ajiye kayayyakin abinci da makamai, wadda sojojin suka ƙone ta.

Waɗanda suka gudanar da atisayen sun haɗa da jami’ai na musamman da daga rundunar jami’in GOC da haɗin-gwiwar wasu sojojin ruwa daga tawagar SBS.

A baya ne dai rundunar sojoji ta ayyana Turji a matsayin ‘gawa mai tafiya’ inda ta yi alwashin ganin bayansa da ayyukansa na ta’addanci a jihohin Zamfara Sakkwato da Neja.

By ukarofi