Shin hoto a Musulunci haram ne?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ 

Musulunci addini ne mai matuƙar wayewa wanda ya zo ya kori jahilci a duniya ta hanyar ilimi, amma da ƙarfin tsiya malamai sun gidadantar da addinin ba don komai ba sai saboda watsi da ginshikin farko da Allah ya gina addinin a kansa na karatu, nazari da bincike domin fahimtar mu’ujizar ubangiji a cikin halittu.

Miliyoyin shekaru kafin a halicci ɗan adam, Allah da kansa ya samar da camera da hoto, wanda daga baya Dan Adam ya kwaikwaya a zahiri. ƙwayar ido ta halittu masu gani, bata da banbanci da tsarin camera, domin camera ta kwaikwayi wannan gwaninta ta ido ne. Sannan hoto kansa, Allah ya fara samar da shi ta hanyar madubi, misali a yanayin haske mai kyau ta hanyar amfani da kwayar ido, idan jaki ya je shan ruwa a rafi sai ya ga surarsa a kan ruwa. Ta hanyar kirkiro gilashi kuma Dan Adam ya sami hanyar kwaikwayar tsarin ubangiji wajen yin madubi da za’a iya tsinkayar sura. Kwayar ido da madubi na bayar da surar hoto mai motsi tamkar bidiyo yayinda kwakwalwa mai tunawa ke samar da hoto mara motsi wato picture. Banbancinsu kawai shine bidiyo na motsi amma hoto baya yi. Daukar hoto a jejjere cikin kasa da dakikoki (frames) shine a dinke ya ke bada ɓideo mai motsi, kamar yadda na ga Sheikh Pantami ya yi kokarin bayyanawa masu cewa hoto Haram ne.

Tunda mun fahimci menene hoto a zahirance, bari mu duba haramcin nasa da wasu ke ikirari. Shin a hankalce, Allah zai haramta abinda ya wajabta a tsarin halittarsa? Kamar yadda na yi bayani a sama, ɓideo da hoto, abubuwa ne da a tsarin halittarmu ke wanzuwa ta hanyar ido da haske, kuma sai Allah ya haramta mana su? Babu aya guda daya kaf a ƙurani da ta haramta hoto, sai dai an haramta sura wadda a ka sassaka da zummar bauta. Misali cikin Suratul Anbiya

Q21:52 & 54 “Ya ce wa ubansa da mutanensa, “Menene wadannan Mutum mutumai (gumaka) da kuke masu lazimta a kansu?”….”Ya ce “Lallai hakika kun kasance ku da ubanninku a cikin bata bayyananniya”

Sannan a suratul A’araf mun ga inda Annabi Musa: Q7:148 “Kuma mutanen Musa su ka riki Dan Maraki, jikin mutane yana ruri, daga bayan tafiyarsa, daga kayan kawarsu. Shin basu gani ba ne cewa lallai shi baya yi musu magana, kuma baya shiryar da su ga hanya, sun rika shi su ka kasance masu Zalunci”

Sassakakken Mutum mutumi domin bauta su ne abubuwa da ƙurani ya haramta. Musulunci ya bayyana a Arabia lokacin da ake tsananin bautar gumaka domin a Ka’aba kawai akwai gumaka 360 sannan kusan kowane gida da nasa gunki. Annabi a kokarin kawar da duk wata bauta ta gumaka ya haramta ajiye duk wata sura a cikin gidajen musulmi. Ya tsoratar a Hadisin Bukhari cewa:

Hadisii: 2:428 “Duk wanda ya yi wata sura, Allah zai masa azaba har sai ya hurawa wannan surar rai, kuma ba zai iya hura mata rai ba”

Sannan ya na kwance cikin ciwon ajali ya ji mata su na tattaunawa a game da coci a habasha

Hadisin Bukhari: 2:425 “Wadannan wadanda idan wani babba ya mutu a tsakaninsu, su ke maida kabarinsu wurin bauta, kuma suke saka surori a wurin. Su ne mafi muni a wajen Ubangiji.”

Wadannan da wasu hadisai na manzo, kamar wanda ke cewa Mala’iku basa shiga gida mai sura, dukkansu na kakkausar suka da haramci ne game da sura ta Mutum mutumi domin kawar da bautar gumaka. 

Wasu malamai ne saboda gurguwar fahimta da rashin fadada tunani, suka dauko wannan fassara ta gunki (sura) suka dora kan hoto na zamani, mai motsi (ɓideo) ko mara motsi (picture). Shi Annabi da mutanen zamaninsa kaf basu san irin wannan hoto namu na zamani ba domin sai bayan shekaru sama da 400, sannan wani musulmi masanin kimiyya, Ibn Al Haytham ya kirkiro camera ta farko a tarihin duniya. Annabi bai san hoto da ɓideo ba ballantana ya haramta su. Allah da kansa, kafin Dan Adam, ya samar da hoto da ɓideo a tsarin halittarmu kuma babu wata aya guda da ta haramta su. Don haka mutane ku sani, Allah da manzonsa ke halastawa ko haramtawa, kuma cikinsu ba wanda ya haramta hoto. Malaman ku ne saboda gurguwar fahimta da rashin sanin ilimin kimiyya su ke haramta muku. Ku sani kuma irin wadannan malamai da su ke gidadantar mana da addini ake ma na kallon jahilai su ne a baya suke cewa muryar mace al’aura ce. 

Malamai ne da a kullum su ke barin jaki su bugi taiki. Musulunci a kullum assasa umarnin a yi, yake yi, amma su kullum sun fi maida hankalinsu a kan bari-bari. Babban burinsu ba na a assasa halal ba ne, sai dai sun fi maida hankali wajen a bar Haram. Sun ba mutane addini a bai-bai. Amru bil ma’aruf gaba ta ke da nahyi domin da zamar mutane sun dabbaka alheri a zukatansu, ba ka bukatar ka ce su bar sharri. Tarihin Musulunci na yadda Annabi ya yi Da’awa ya nuna haka. Tsarin koyarwar ƙurani a shekarun Makka kafin hijira ya nuna haka. Amma malamanmu ba ruwansu da ginshikin addini, misali tilasta Zakka, amma idonsu na kan laifuka, yadda idan kana duba maganar shari’ar Musulunci sai kaga ana daukar aiwatar da haddi kawai shine shari’a. Ko Allah zaka ga ya fi jaddada “Amana bil lah, wa amila salihan” a ginshikin samun tsira, wato a kullum yin alheri shine gaba, amma sai Malamai su ka mayar da shi baya, su ka tunkudo hani gaba. Shi yasa musulmin zamani na ta kyamatar sharri amma aikata alheri ya gagaremu. Da alheri muka saka gaba, da tuni mun cinye sharri da yaki. 

A ƙarshe, duk malamin da ya yarda cewa hoto Haram ne, to don Allah ya kauracewa mu’amala da duk wata harka da ta jibanci hoton (camera, Tɓ, passport, ID da sauransu). Mu Kuma ya bar mu da ci gaba da mu’amalarmu da abinda mu ka yadda halal ne, saboda daga Allah har Annabi babu inda mu ka ga sun haramta mana su.

Ali Abubakar Sadiƙ manazarci ne kuma marubuci a birnin Kano