
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce, jagoranci na gari da hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu zai taimaka wajen sauya Nijeriya ta fuskar samun ci-gaba a nan gaba.
Ya ce, hakan zai samu ne la’akari da ƙoƙarin da ya ke yi na zuba jari a ƙarƙarshin tsarinsa na sabonta ƙasa a ɓangarorin kiwon lafiya, Ilimi da wasu manyan ababen harkar tattali.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ya karɓi baƙoncin tawagar Gidauniyar Big Win Philanthropy kaseta A, ƙarƙashin jagorancin Shugabarta, Jamie Cooper a Fadar Shugaban ƙasa, a Abuja.
Ya kuma marabci buƙatar gidauniyar ta neman yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da gwamnatin Shugaba Tinubu don cimma manufofin Ajendarsa ta Sabonta ƙasa, ya na mai cewa a shirye suke su bada duk haɗin kan da ake buƙata wajen cimma nasara.
Haka kuma, ya bayyana shirin ‘Nutrition 774 Initiative’ a matsayin abinda zai amfani al’umma tun daga mataki na ƙananan hukumomi don yaƙi da rashin samun wadataccen kulawa a ɓangaren lafiya.

A nata jawabin, Shugabar Gidauniyar, Cooper, ta ce sun ziyarci Fadar shugaban ƙasar ne da nufin tattaunawa da mataimakin shugaban ƙasar ganin yadda ya ke taka muhimmiyar rawa a ayyukan inganta ƙasa da al’umma da kuma neman haɗa hannu da gwamnati don cimma kyawawan manufofinta.
