Shugaba Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta magance matsalar wutar lantarki a fannin lafiya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta magance matsalolin da ake fama da su a ɓangaren lafiya a Nijeriya ta hanyar samar da sauyi a ɓangaren samar da wutar lantarki.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a lokacin da yake gabatar da jawabi wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan samar da lantarki a ɓangeren lafiya.

Taron wanda na kwana biyu ne, an yi masa take ne da: “Samar da wutar lantaki ta hanyar haɗa kai da gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin gobe”.

Shugaban ƙasa ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya ne, George Akume, wanda ya ce shugaban ƙasa ya ce, gwamnatinsa za ta magance matsalar ƙarancin wuta a ɓangaren lafiya.

Ya kuma ce matsalar wuta na ƙara tsadar neman lafiya da katsewar ba da kulawa da inganci da rashin samun gamsuwa daga marasa lafiya.

Sannan ya jaddada aniyar inganta damar samun makamashi ga asibitoci a matsayin wani ɓangare na sabunta fatan Nijeriya.

“Ta tsarin kawo sauyi a ɓangaren makamashi, gwamnatinmu na ƙoƙarin kawo sauyi ta hanyar samar da tubalin kyakkywan tsarin rarraba makamashi a faɗin Nijeriya,” ya faɗa.

Shugaban ƙasa ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta faɗaɗa samar da wutar sola a ayyukan more rayuwa na al’umma wanda hakan zai ba wa kamfanoni masu zaman kansu damar shigowa a dama da su. Kuma ya ce, za a samar da kyakkyawan tsari na haɗakar gwamnati da kamfanonin masu zaman kansu (PPPs) domin tallafa bunƙasa makamashi mai ɗorewa.

“Wannan tattaunawa bai kamata ta ƙara a matsayin zance ba kawai,” ya faɗa.

“Ya kamata ta haifar da sakamako da za su yi daidai da gwamnatin tarayya da na jihohi wajen ɗaukar nauyi da tsarin bibiya domin tabbatar da an cimma abin da ake fata.”

Shi ma ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce ma’aikatar ta hannun hukumar samar da wutar lantarki a karkara (REA) ta samar da ƙananun tashohin wuta da sanya wutar haskaka gidaje da sauran nau’o’in makamashi sabuntau wajen tabbatar a wutar lantarki a asibitocin da ke karkara a faɗin Nijeriya.

Ya kuma tuna cewa a lokacin Kwabid-19, an samar da tashar wutar sola mai girman 50kW a asibitoci 100 domin tabbatar da wuta marar yankewa don cigaba da hidimta wa al’umma.

“Wannan ya haɗa da tashar wutar sola mai girman 12MW da aka saka a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da wata mai girman 7MW a asibitin koyarwa na jami’ar Calabar.

Shi ma ƙaramin ministan lafiya da walwala, Iziaƙ Salako, ya ce, wani bincike ya nuna cewa kaso 40% na asibitoci a matakin farko ba su da wadatacciyar wutar lantarki.

Salako ya ƙara da cewa akwai makarantun gwamnatin tarayya da ke kashe tsakanin Naira miliyan 20 da Naira miliyan 180 wajen biyan kuɗin wuta duk wata wanda ya ki kaso 50% na kuɗin gudanar da asibitocin.

“ɓangaren lafiyarmu ba kaɗai yana fama da rashin wuta ba ne, har ma da rashin wuta mai inganci. Rashin lantarki ya zama babban ƙalubalen da ke kawo tsaiko a fannin lafiya.

“Tilas ne a gaggauta kawo gyara a fannin lafiya,” ya faɗa.

Salako ya ce ana buƙatar sauya ɗaukacin tsarin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu ne ta hayar zuba jari saboda gwamnatin kaɗai ba za ta iya samar da wuta a ɓangaren lafiya ba.

Ministan lafiya da walwa, Muhammad Pate, ya nuna muhimmancin samar da wuta da intanet domin kawo sauyi a fannin samar da wuta a asibitoci.

“Idan za mu iya gyara matsalar lantarki da intanet, to za mu iya inganta fannin lafiyarmu,” Pate ya faɗa.

Ya ce, abin da ke ciwa ɓangaren lafiya tuwo a ƙwarya shi ne rashin kuɗin da ake kashewa inda ya yi kira da a samu haɗin guiwa da ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa an kammala taron tattaunawar ce a rannar Laraba da nufin haɗa kai a mataki na ƙasa domin magance matsalar makamashi a ɓangaren lafiya a faɗin Nijeriya.

By ukarofi