Shugaban Amurka ya kira Tinubu yana godiya bisa sakin Shugaban Binance

Daga USMAN KAROFI

Shugaban Amurka, Joe Biden, ya miƙa godiyarsa ga Nijeriya da Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata bisa sakin babban jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan.

Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana wannan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban Ƙasa game da tattaunawar minti 30 da aka yi tsakanin shugabannin biyu ta waya.

“Ina sanar da ku bisa umarnin Shugaban Ƙasa dangane da hirar wayarsa da Shugaban Amurka Joseph Biden da misalin ƙarfe 4 na yammacin yau.

“Shugabannin biyu sun yi musabaha sannan Shugaba Biden ya godewa Shugaba Tinubu bisa haɗin kai, musamman kan goyon bayan Nijeriya wajen sakin ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi daga kamfanin musayar kirifto da muka sani,” in ji Tuggar.

Gambaryan ya bar Nijeriya a ranar Litinin bayan tsarewar wata takwas bisa doka, kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

“A yau, ɗan kasar Amurka Tigran Gambaryan ya bar Najeriya don komawa gida ga iyalansa bayan wata takwas na tsarewa ba bisa ƙa’ida ba,” a cewar wata sanarwa daga iyalansa.

Gambaryan, babban jami’i a kamfanin Binance, an kama shi a farkon shekarar 2024 a Nijeriya yayin wani matakin murƙushe harkokin kirifto da gwamnatin Nijeriya ta ɗauka.