Shugaban Malawi ya jinjina wa matakin Ƙasar Sin na yafe wa ƙasashen Afirka basussuka marasa ruwa

Daga CMG Hausa

Shugaban ƙasar Malawi Lazarus Chakwera, ya jinjinawa matakin ƙasar Sin, na yafe wa wasu ƙasashen Afirka 17, basussuka marasa ruwa da take bin su.

Da yake bayyana hakan a ranar Alhamis, a gefen babban taron MƊD karo na 77 dake gudana, shugaba Chakwera ya ce “Na yabawa ƙasar Sin bisa yadda take jagoranci abun misali, inda ta cika alkawarin da ta ɗauka yayin taron dandanlin raya haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka na FOCAC da ya gudana a bara, na yafewa ƙasashe Afirka 17 bashi maras ruwa da take bin su”.

Shugaban na Malawi ya ƙara da cewa, ya kamata a cika alƙawarin yin tafiya tare da kowa, a kuma yi hakan a fayyace, ba wai ta maganar fatar baki kaɗai ba.

Ya ce “Idan har mu iyali guda ne na MƊD, ya zama wajibi mu ajiye batun siyasa, mu rungumi ƙarin tallafi wajen warware matsalolin mu”.

Mai fassara: Saminu Alhassan